An yi garkuwa da , Eze Charles Iroegbu, basaraken Umueze da ke yankin Nguru a karamar hukumar Aboh Mbaise a jihar Imo.
’Yan bindigar sun yi garkuwa da basaraken da fadawansa ne a kan titin Mbano zuwa Mbaise, yayin da suke kan hanyar dawo wa daga wani bikin gargajiya da suka halarta a ranar Laraba .
- Damfarar N450m: Kiristoci sun fi Musulmi tausayi —Ummi Zee-zee
- Ya kashe masoyiyarsa da ’ya’yanta saboda ta rabu da shi
- WAEC ta fitar da sakamakon jarabawar 2021
Zuwa wannan lokaci na hada wannan rahoton ba a bayyana adadin fadawan da aka sace yayin garkuwa da basaraken ba.
Wata majiya a Nguru, ta bayyana cewa lamarin ya jefa mazauna yankin sun shiga cikin dimuwa.
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin kakakin ’yan sandan jihar, SP Orlando Ikeokwu, sai dai hakar ba ta cimma ruwa ba.