’Yan bindiga sun sa garin Kaduna a tsakiya, lamarin da ya haddasa karuwar ayyukan garkuwa da mutane a garuruwa da kauyukan da ke kusa da garin.
Daruruwan mutane da suka kaurace wa gidajensu a yankunan a wajen garin Kaduna saboda ayyukan ’yan bindiga suka dawo kusa da garin Kaduna sun shaida mana cewa ’yan bindigar na ci gaba da bibiyar su a inda suka dawo.
- Kwastam ta kama wukake da tabar wiwin N10.4m a Kaduna
- NAJERIYA YAU: Za a koma biyan kudin haya wata-wata a Abuja
A baya-bayan nan ’yan bindiga sun yawaita kai hare-hare a gidaje da kauyukan da ke kusa da garin Kaduna, wanda ya sa ake fargabar cewa tsaurin idonsu na kara karuwa.
Sai dai wasu majiyoyin tsaro sun shaida mana cewa rikicewa ’yan bindigar suka yi saboda uzzura musu da jami’an tsaro suka yi da hare-hare a maboyarsu da ke cikin daji, shi ya sa suka koma kai hari a cikin al’ummomi da ke kusa da garin Kaduna, domin guje wa shiga hannun jami’an tsaro.
Yanzu dai kusan shekara 10 ke nan da ayyukan ’yan bindiga ya fara raba mutane da dama da muhallansu a yankin Kaduna ta Tsakiya.
Tun a shekarar 2013, Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari, ya bayyana kokensa game da ayyukan ’yan bindga da ke mamaye wasu yankuna da ke karkashin masarautarsa.
Daga baya ayyukan bata-garin suka rika watsuwa zuwa Kananan Hukumomin Chikun, Igabi, Giwa da kuma Zariya, a baya-bayan nan.
A bisa binciken da muka gudanar a makonnin baya-bayan nan, mun gano cewa a ’yan watannin nan, an samu karuwar aikata miyagun laifuka a yankin Birnin Kaduna, musamman a birnin Zariya, da kuma garuruwan Birnin Gwari da Giwa.
A baya wadannan yankuna su ne suka kasance mafaka ga mutanen da suka gudo daga yankunansu saboda yadda ’yan bindiga suka fitine su.
‘Kaduna babu tsaro’
Wasu mazauna Kaduna da muka zanta da su sun bayyana damuwarsu kan yadda ’yan bindiga suke kai hare-haren a yankunan da nisansu bai fi kilomita biyar daga kwaryar birnin Kaduna ba, irin su Rigachikun, Rigasa, Barakallahu, Narayi Layout, Gbagi Villa, Maraban Rido da kuma Sabo.
Birnin Kaduna wanda ke da fadin murabba’in kilomita 2,231.41, ya kunshi kananan hukumomin Kaduna ta Arewa, Kaduna ta Kudu, Chikun da Kuma Igabi, kamar yadda gwamnatin jihar ta ayyana a watan Oktoban 2021.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar mana cewa a ’yan makonnin da suka gabata, ’yan sanda sun sun dakile wani yunkurin garkuwa da mutane a unguwar Sabon Kawo da ke kwaryar Birnin Kaduna.
Mjiyarmu ta ce, ’yan bindigar sun ritsa wasu iyalai suna so su yi garkuwa da su, amma ’yan sanda suka kawo dauki, inda suka yi musayar wuta da maharan har suka kwato bindiga kirar AK-47 guda daya daga wurin ’yan bindigar.
Da yake bayani kan karuwar hare-hare a Birnin Kaduna, wani masanin sha’anin tsaro, Dokta Awwal Abdullahi Aliyu, ya ce hakan wata alama ce da ke nuna cewa babu wanda ya tsira daga hadarin.
Ya ce alamu sun bayyana karara cewa ’yan ta’adda sun samu karfin gwiwar da har suke iya shiga cikin manyan garuruwa kamar garin Kaduna su kai hari.
Ya bayyana cewa, “An riga an bayyana ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda, su kuma ’yan ta’adda suna iya yin kowace irin kasada domin samun biyan bukatarsu.
“Sun yi nasara wajen sanya tsoro a zukatan mutane da kuma tilasta wa mutane baro wajen gari su taru a wuri daya.
“Wannan kuma babban hadari ni. Yanzu wadansunsu na zaune a cikin al’umma domin su rika samun bayanai; Saboda haka ya kamata jami’an tsaro su bullo musu ta wata sabuwar hanya.”
Dokta Auwal ya yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro da kuma mazauna da su kafa cibiyoyin tsaro da tara bayanai da kuma bayar da su da sauri.
A baya-bayan nan ne Gwamnatin Jihar Kaduna ta fitar da rahoton da ke nuni da cewa ’yan bindiga da sauran matsalolin tsaro sun yi sanadiyyar kashe mutum 1,192 tare da yi garkuwa da wasu 3,348 a jihar a shekarar 2021.
Daga cikin adadin, mutum 720 an kashe su ne a yankin Kaduna ta Tsakiya, inda aka sace mutum 2,771.