✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe sojojin Najeriya 20 a Neja

Sojojin Najeriya kimanin 20 ne ’yan bindiga suka kashe a wani harin kwanton bauna a kan hanyar Zungeru zuwa Tegina da ke Jihar Neja.

Sojojin Najeriya kimanin 20 ne ’yan bindiga suka kashe a wani harin kwanton bauna a kan hanyar Zungeru zuwa Tegina da ke Jihar Neja.

Majiyarmu ta shaida mana cewa an kai karin sojoji bakwai da ’yan banga biyar da suka samu raunuka a harin zuwa Asibitin Kwararru na IBB da ke Minna, babban birnin jihar.

Wata majiyar soji ta tabbatar mana cewa daga cikin sojoji 20 da suka rasu a harin na ranar Lahadi da dare, akwai sojojin kasa guda 18 da kuma sojojin sama biyu.

Majiyarmu ta ce ’yan bindigar sun kai harin ne a lokacin da sojojin ke hanyarsu ta zuwa wasu kauyukan Karamar Hukumar Wushishi ta jihar da mahara suka kai wa farmaki.

Harin da ’yan bindiga suka kai wa kauyukan a ranar Juma’a ya tilasta wa mazauna, wadanda galibinsu manomna ne tserewa zuwa yankunan Wushishi da kuma Zungeru.

Yadda abin ya faru

Wata majiya ta ce ’yan bindigar suna tsallaka babban titin Zungeru-Tegina tare da dimbin shanun da suka sace daga kauyen Kudu da ke Karamar Hukumar Rafi ta jihar ne “suka yi arba da sojojin da aka tura, inda suka fara musayar wuta da ya yi ajalin sojojin.”

Wani mazaunin garin ya ce: “Gaskiya ne, an yi musayar wuta tsakanin sojoji da ’yan bindiga a wajen kauyen Kundu, a ranar Lahadi,“ amma ta ce sojoji 12 ne aka kashe.

Sanatan da ke wakiltar yankin, Mohammed Sani Musa, ya tabbbatar mana a Abuja ranar Litinin, amma ya ce sojoji 13 ne aka kashe, inda ya roki Gwamnatin Tarayya ta tura karin sojoji don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoin al’ummar yankin.

‘Murna ta koma ciki’

Sanata Musa ya ce: “Wannan babban al’amari ne a daidai lokacin muka fara farin ciki cewa ayyukan ’yan bindiga sun ragu a Jihar Neja.

“Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin gaggawa na tura matakan tsaro domin hana yaduwar wannan abu.

“A baya an samu raguwar hare-haren amma yanzu abin yana ta karuwa, kuma abin damuwar shi ne na yanzu kamar kitsawa ake yi, idan aka dubi yadda maharan ke kai hari lokaci guda a wurare daban-daban a Jihar Neja.

“Muna rokon gwamnati, don Allah ta gaggauta daukar kwararan matakai domin kare rayuka da dukiyoyyin mutanenmu,”  in ji shi.

Tsuguno ba ta kare ba –Matasa

Jagoran Kungiyar Mata Masu Kishin Yankin Shiroro, Sanni Kokki, ya shaida mana ta wayar tarho cewa “an yi wa sojoji kwanton bauna aka kashe 13 a hanyar Zungeru zuwa Tegina da ke Karamar Hukumar Rafi.

“Maganar nan da muke yi, mazauna wadannan kauyuka sun fara yin kaura zuwa yankin Erena.

“Wannan sabuwar matsala ce da ke raba mutane da garuruwansu na iyaye da kakanni zuwa inda ba su sani ba, wanda wannan kari ne a kan matsalar tattalin arziki da ake fama da ita.”

Jirgin yaki ya fadi a Neja

Kakakin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Iya Komodo Edward Gabkwet, ya tabbatar da faduwar wani helikwaftan rundunar samfurin MI-171 a yayin da yake aikin kwashe mutane a ranar Litinin a kauyen Chukuba da ke jihar ta Neja.

Sanarwar da ya fitar ba ta bayyana adadin ma’aikatan da ke cikin jirgin ba, ballantana ko an samu asarar rai, duk da cewa ana hasashen fasinjojin za su kai mutum 20.

Amma ya ce ana kokarin ceto jami’ai da fasinjojin helikwaftan, kuma an fara gudanar da binciken farko domin gano ainin abin da ya faru.

Sai dai wasu rahotanni da ba mu iya tabbatarwa ba suna riya cewa ’yan ta’adda ne suka harbo helikwaftan, kuma matukinsa ya kwanta dama.

Iya Komodo Gabkwet ya bayyana cewa jirgin ya fado ne bayan ya taso daga Makarantar Firamaren Zungeru zuwa Kaduna, amma sai ya fado a kusa da kauyen Chukuba da ke Shiroro.

Sojoji sun ki cewa komai

Zuwa lokacin kammala wannan rahoto dai Hedikwatar Tsaron Najeriya ba ta ce komai a kan batun kashe dakaruntta ba.

Mun tura wa mai magana da yawun hedikwatar tsaron, Manjo Janar Edward Buba rubutaccen sakon neman karin bayani amma babu amsa ba. Kafin haka, wakilinmu ya kira wayansu ba sau daya ba, amma bai dauka ba.

Amma wani hafsan soji da ya bukaci kada mu bayyana sunansa, ya tabbatar mana cewa sama da sojoji takwas aka kashe a harin.

“Abin takaici ne, wasu abokan aikinmu sun gamu da ajalinsu a harin karshen mako. Ba zan iya fadan hakikanin adadin su ba, amma na san sun fi mutum takwas da aka kashe,” in ji shi.

A shekarar da ta wuce ’yan bindiga sun kashe sojoji 15 da yan sanda bakwai a Jihar Neja. Wasu mazaunan yankunan sun yi zargin maharan sun samu taimakon wasu bata-gari a kauyukansu.

Shugaban Karamar Hukumar Shiroro, Akilu Isyaku Kuta, ya shaida wa wakilinmu a ranar Litinin cewa sha’anin tsaro ya fara kara tabarbarewa a yankinsa.

 

Daga Sagir Kano Saleh, Idowu Isamotu, Abdullateef Salau (Abuja) da Abubakar Akote (Minna).