’Yan bindiga sun hallaka mutane 96 tare da kona gidaje 221 a wasu kauyuka 15 a kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi da ke Jihar Filato.
Da yake tabbatar da harin a safiyar Talata, kakakin yan sandan jihar, DSP Alfred Alabo ya ce ’yan bindigar sun lalata motoci takwas da babura 27 a harin na a ranar Lahadi — jajibirin Kirsimeti
DSP Alabo ya sanar a garin Jos cewa “da misalin karfe 10 na daren Lahadi 24 ga Disamba ne mahara suka kai wa kauyuka 15 farmaki a lokaci guda a kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi.
“Kauyuka 12 aka kai wa hari a Bokkos, inda aka kashe akalla mutane 79 aka kona gidaje 221 da babura 27 da motoci takwas.
- Mutum 4 sun mutu, 59 sun jikkata a hatsarin mota a hanyar Abuja
- Matashin Da Zaman Gidan Yari Ya Zame Wa Alheri
“A Barkin-Ladi kuma kauyuka uku aka kai wa farmaki inda aka kashe rayuka 17.
“Ana ci gaba da bincike da sintiri kuma duk abin da aka gano za a sanar da jama’a,’’ in ji DSP Alabo, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito.
Kauyukan Karamar Hukumar Bokkos da aka kai wa hari, a cewarsa, su ne: Ndun, Ngyong, Murfet, Makundary, Tamiso, Chiang, Tahore, Gawarba, Dares, Meyenga, Darwat da kuma Butura Kampani.
Wadanda aka kai wa hari a Barkin-Ladi kuma su ne NTV, Hurum da Darawat.