✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ’yan bindiga suka kashe mutum 15 a hanyar Kaduna

Maharan da suka yi ta harbin motoci ba kakkautawa sun yi garkuwa da mutane da dama

’Yan bindiga sun kashe akalla mutum 15 suka kuma yi garkuwa da wasu da dama a kan hanyar Abuja-Kaduna a yammacin Lahadi.

Shaidu sun ce lamarin ya auku ne a kusa da kauyen Gidan Busa daura da Rijana mai tazarar kilomita 133 daga Abuja da misalin karfe biyar.

Wani ganau ya ce, “Bas biyu da wata wagon da ke gabanmu aka fara bude wa wuta; ta farkon ta yi ta tangaltangal a kan hanya kafin daga baya ta tsaya”.

Akalla motoci 20 ne suka fada hannun ’yan bindigar da suka yi musu kwanton bauna a daidai wurin da hanyar ta lalace a kusa da kauyen.

Shaidu sun tabbatar wa Aminiya cewa babu alamar jami’an tsaro a yankin lokacin da masu garkuwar suka kai farmakin.

Sun shaida wa wakilinmu cewa baya ga mutm 15 da aka kashe, an yi awon gaba da wasu da dama, ciki har da mata da kananan yara.

Aminiya ta tuntubin Kakain Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Mohammed Jagile amma ya ce zai tuntube mu daga baya domin a lokacin Baturen ’Yan Sanda mai kula da yankin na kan hada rahoton abin da ya faru.

Yadda abin ya faru

Ganau sun shaida wa Aminiya cewa masu garkuwa da mutanen sun kai harin ne dauke ne da manyan bindigogi suna harbin motocin da ke hannun da ke zuwa Abuja daga Kaduna.

’Yan bindigar sun tare hanyar ne suka yi ta harbi wanda hakan ya tilasta wa motocin tsayawa suka kuma bindige wasu daga cikin matafiyan da suka yi yunkurin tserewa.

“Motar da aka fara kai wa hari bas ce mai daukar mutum 18 cike da fasinjoji”, wani shaida da ke hanyarsa ta zuwa Katsina daga Abuja mai suna Mamman ya shaida wa wakilinmu ta waya.

“Ina daga cikin wadanda suka tsira; na ga duk abin da ya faru na kuma taimaka wajen kwashe gawarwakin daga kan hanya”, inji Maman.

Ya ce harsashi ne ya sami direbar bas din kirar Hummer ya kashe shi nan take wanda hakan ta sa motar ta yi ta tangaltangal kafin daga baya ta tsaya a tsallaken titin.

“Motoci uku ne a gaban tamu lokaicn da muka ga kwatsam masu garkuwar sun fito kan hanyar sun fara harbi babu kakkautawa.

“Bas biyu da wata wagon da ke gabanmu aka fara kai wa hari aka bude musu wuta; ta farkon ta yi ta layi a kan hanya kafin ta tsaya.

“Abin ya kuma shafi wata Hummer ta biyu da wata saloon, motarmu  Volkswagen Golf ce hudu; da direbanmu ya ga abin da ke faruwa sai ya sauka daga kan titi”, inji Mamman.

Ya ce, “Motocin da ke zuwa daga baya, ina jin za su kai 20 dole suka tsaya; fasinjoji da dama cikin tashin hankali har da wasu na cikin motarmu sun tsere.

“Ban san abin da ya hana ni guduwa ba, kawai matsawa kusa dakaliln tsakiyar titi na labe kuma na ga lokacin da suka kora mutanen da suka yi garkuwa da su cikin jeji,” kafin daga baya ’yan sanda su zo, inji shi.

“Wasu ’yan sanda sun kawo mana dauki kuma na taimaka wurin gano wadanda aka kashe da wadanda suka samu rauni.

“’Yan sanda da wasu mutane sun kawar da motocin da suka tare hanya kafin aka fara wucewa, na sauka a hanyar Abuja ne saboda ta Bwari zan bi”, inji shi.

Shi ma wani mazaunin yankin, Malam Mu’azu, ya tabbatar wa wakilinmu cewa an kai harin a kan hanyar ta Abuja-Kaduna.

“Ba na wurin da aka kai harin amma wani wanda na sani da ya bi ta wurin ya ce ya ga abin da ya faru.

“Wannan hanar (Abuja-Kaduna) ta sake komawa mai matukar hadari. Watannin baya jami’an tsaro sun matsa kaimi a kan masu garkuwa da mutane amma yanzu kamar sun yi barci.

“Gaba daya yankin Jere mai nisan kusan kilomita 70 daga Abuja babu tsaro; yanzu masu garkuwa kan yi wa mutane kwanto tun daga Kurmin Kare, Gidan Malam Mamman har zuwa Rijana”, inji mutumin.

A kan hanyar akwai wata babbar cibiyar tsaro da aka girke a kauyen Katari mai nisa kilomita 92 daga Abuja.

An girke jami’an tsaro da suka hada da masu yaki da satar mutane, ’yan sanda, sojoji, Civil Defence da sauransu a yankin na Katari.

Suna girke a wurin ne domin su rika kai dauki a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Mazauna yankin sun jaddada bukatar a sake bincikar dawowar masu garkuwa da mutane a kan hanyar wadda ita ke sada yankin Kudancin Najeriya da Abuja da kuma yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.

An kashe daruruwan mutane tare da garkuwa da wasu wadanda iyalansu suka biya makudan kudaden fansa domin kubutar da su daga hannun masu garkuwa.