✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ’yan bindiga suka kashe mijina wata daya da aurenmu

Sun mayar da ni mai takaba bayan bindige mijina a gabana.

Wata mata mai suna Ramatu Idris a yankin Dutsen Abba na Karamar Hukumar Zariya, Jihar Kaduna ta bayyana yadda ’yan bindiga suka kashe mijinta, wata bayan aurensu.

Ramatu ta ce a gabanta masu garkuwa da mutane suka bindige angonta Suleiman, kwanaki kadan da yin bikinsu.

“Wajen su bakwai ne suka shigo gidanmu dauke da bindigogi da sanduna.

“Ni da mijina muka fita don ganin me ke faruwa da muka ji hayaniya, a gabana suka harbe shi a wuya, kuma nan take ya rasu,” a cewar Ramatu wadda a halin yanzu take kan takaba.

Ta bayyana a cikin damuwa ’yan bindigar da suka kashe mijinta ne suka kutsa gidan Kansilan Dutsen Abba, Alhaji Abdulaziz Sani suka yi garkuwa da mutum shida daga cikin iyalan Kansilan.

Zatar ta ce bayan yin garkuwa da iyalan Kansilan, ’yan banga sun yi nasarar cafke wasu daga cikinsu a kauyen Mai Turmi da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Mazauna gundumar Dutsen Abba, sun roki Gwamnatin Jihar Kaduna da ta samar musu da jami’an tsaro da za su kare su hare-haren ’yan bindiga.