Mutum tara sun bakunci lahira a hare-haren da ’yan bindiga suka kai a wasu kananan hukumomi hudu na Jihar Kaduna.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan, ya ce hare-haren sun auku ne a kananan hukumomin Chikun, Zangon Kataf, Igabi da kuma Zariya.
- Yadda sojoji suka ragargaji Turji da yaransa a Sakkwato
- An kama bindigogi 35 da masu muggan laifi 245 a Kano
Aruwan ya sanar a ranar Juma’a cewa ’yan bindiga sun kashe mutum uku tare da jikkata wani a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna da ke Karamar Hukumar Chikun, a tsakanin kauyen Buruku-Udawa.
A cewarsa, wanda ya samu raunin na samun kulawa a wani asibiti.
Mahara sun kuma kashe mutum daya a yankin Yola-Kadi da ke karamar hukumar, inda a nan ma suka jikkata mutum daya.
Sun kuma kashe mutum biyu a kauyen Sako da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf inda aka gano gawarwaki biyu a yankin Kurfi-Magamiya.
A karamar Hukumar Zariya kuma an kashe wani magidanci a kauyen Saye.
Ya bayyana damuwar gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, gami da addu’arsa ta samun rahama ga mamatan da kuma sauki da wadanda suka samu rauni.