✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ’yan bindiga suka guntule hannayen wani a Zamfara

Yanzu haka ni da Yayana muna kwance a asibiti saboda nima na samu karaya a hannu da kafa.

Wasu ’yan bindiga sun yanke hannayen wani mutum mai suna Samaila Muhammad a Karamar Hukumar Kauran Namoda ta Jihar Zamfara.

An kai wa wanda aka yankewa hannayen hari ne bayan ’yan bindigar sun kutsa cikin gidansa da ke Unguwar Walo a karamar hukumar.

Dan uwan ​​wanda abin ya shafa, Abdullahi Mohammed, wanda shi ma ya samu rauni a yayin harin, ya bayyana yadda aka sare hannayen dan uwansa biyu.

“Yanzu haka ni da Yayana Samaila muna kwance a asibiti saboda nima na samu karaya a hannu da kafa.”

“Da misalin karfe 11:30 na dare ne ‘yan bindigar suka kai mana hari bayan sun shigo cikin gidanmu da farfin tsiya.

“Suna shigowa suka fara neman inda muka ajiye dabbobinmu.

“Hakan ya sa muka fara jin hayaniya muka kunna fitilunmu muka fito daga dakunanmu domin gano abin da ke faruwa.

“Na ga daya daga cikinsu mai dauke da makami yana kokarin kora kajinmu, sai na haske shi da fitila.

“Ya yi harbi inda ya hangi hasaken fitilar, duk da cewa harsashin bai iya samuna ba. Na yi saurin matsawa daga inda na tsaya.

“Sai suka fara tattara kajinmu, lokacin da yayana ya tunkare su, sai daya daga cikinsu ya fito da adduna ya sare hannunsa guda, kafin ya yi yunkurin tserewa, har ya sare masa daya hannun.

Ya kara da cewa, “Al’ummarmu sun sha fama da munanan hare-hare a baya kuma mun sha wulakanci da dama ciki har da fyade da ake yi wa mata.

“A halin yanzu muna karbar magani kuma muna samun sauki bayan mun shafe kwanaki a wurin jinya.”