✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ’yan banga suka hallaka ’yan bindiga 20 a Taraba

Sun bin ’yan bindigar maboyarsu, inda suka suka kashe akalla 20 sauran kuma suka tsere da raunukan harbi a jikinsu.

Akalla ’yan bindiga 20 ne ’yan banga suka hallaka a wani gumurzu da suka tafka a Karamar Hukumar Gassol ta Jihar Taraba.

An yi gumurzun ne bayan ’yan bangar sun bi ’yan bindigar har  maboyarsu da ke cikin daji, suka kashe 20 daga cikinsu a musayar wuta.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa ’yan bangar sun rutsa ’yan ta’addar ne a wani daji da ke kusa da Gassol, inda aka dauki kusan awa uku ana musayar wuta a tsakaninsu.

Sai dai kuma mutum biyu daga cikin ’yan bangar sun kwanta dama a sakamakon artabun na ranar Talata.

Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindiga sun addabi yankin da sace mutane da yi watan aure fyade na tsawon lokaci, amma an yi nasarar kashe da dama daga cikinsu a lokacin gumurzun.

“’Yan bindiga sun sace mutane sama da dari sannan sun sace dabobbi babu iyaka,” a cewar majiyar.

An kuma ruwaito cewa ’yan bangar sun lalata maboyar da ’yan bindigar suke ajiya mutanen da suka yi garkuwa da su.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin ’Yan Sandan Jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya ce, “An kashe ’yan bindiga da dama, sannan wasu sun tsere da muggan raunukan harki, kazalika ’yan banga biyu sun rasa mutum biyu daga cikinsu.”