Akalla ’yan bindiga 20 ne ’yan banga suka hallaka a wani gumurzu da suka tafka a Karamar Hukumar Gassol ta Jihar Taraba.
An yi gumurzun ne bayan ’yan bangar sun bi ’yan bindigar har maboyarsu da ke cikin daji, suka kashe 20 daga cikinsu a musayar wuta.
- Kasar Girka ta ba wa Najeriya tallafin rigakafin COVID-19
- AFCON 2021: Najeriya ta yi wa Masar ci 1 mai ban haushi
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa ’yan bangar sun rutsa ’yan ta’addar ne a wani daji da ke kusa da Gassol, inda aka dauki kusan awa uku ana musayar wuta a tsakaninsu.
Sai dai kuma mutum biyu daga cikin ’yan bangar sun kwanta dama a sakamakon artabun na ranar Talata.
Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindiga sun addabi yankin da sace mutane da yi watan aure fyade na tsawon lokaci, amma an yi nasarar kashe da dama daga cikinsu a lokacin gumurzun.
“’Yan bindiga sun sace mutane sama da dari sannan sun sace dabobbi babu iyaka,” a cewar majiyar.
An kuma ruwaito cewa ’yan bangar sun lalata maboyar da ’yan bindigar suke ajiya mutanen da suka yi garkuwa da su.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin ’Yan Sandan Jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya ce, “An kashe ’yan bindiga da dama, sannan wasu sun tsere da muggan raunukan harki, kazalika ’yan banga biyu sun rasa mutum biyu daga cikinsu.”