A watan jiya ne labarin wani mutum mai suna Malam Sa’idu Abdullahi wanda ya fito daga kauyen Dakatsalle a Karamar Hukumar Bebeji a Jihar Kano, ya mamaye kafafen watsa labarai na ciki da wajen Najeriya, lokacin da ya koma gida bayan an yanke kauna kan yana raye sama da shekara 60.
Mutumin, wanda ya bar gida yana da shekara 26 don zuwa ci-rani a Kudu, ya koma gida ne bayan ya tsufa sosai. Sai dai ba wannan mutum ne kawai ya yi irin wannan rayuwa a Kudu ba, akwai dimbin ’yan Arewa da suka yi ban-kwana da garuruwansu kuma suka yi zaman dirshan shekara da shekaru ba tare da sun leka gida ko da sau daya ba. Akasari irin wadannan mutane sukan rayu su mutu a wani mugu yanayi. Aminiya ta kara bin sawun irin wadannan mutane inda ta samo karin wadansu mutanen da suka yi wa Kurmi shiga sojan Baddakare:
Shekarata 55 rabona da Arewa – Najume Garba
Wani dattijo mai kimanin shekara 65 zuwa 70 mai suna Najume Garba wanda aka fi sani da Baba Iwuru wanda yanzu haka yake zaune a wani kauye mai suna Akampa a Jihar Kuros Riba da ke Kudu maso Kudu, ya shaida wa Aminiya cewa ya shafe kusan shekara 55 yana zaune a Kudu ba tare da ya leka gida Arewa ba.
Najume ya ce bacin rai ne ya raba shi da garinsu na asali a Karamar Hukumar Mai’aduwa da ke Jihar Katsina, inda ya tafi Kurmi tun yana dan kimanin shekara 16 a duniya.
Dattijon wanda ya ki fadin sunan kauyensu na asali a Jihar Katsina, kuma ya ki yarda a dauki hotonsa, ya shaida wa wakilinmu cewa: “Bacin rai a tsakanina da ’yan uwana da muke ’yan uba ya sanya na bi dare na baro kauyenmu kimanin shekara 55 da suka gabata.
Ya ci gaba da cewa da farko garin Enugu ya fara zama, “Lokacin ina matashi majiyin karfi ana zuwa Enugu da Jos aikin kuza sai na bi ayarin mutanen da za su je aiki. Da yake muna da yawa sai aka raba mu biyu wadansu aka tafi da su Jos, ni kuma aka tura ni Enugu. Ina can ina aiki, sai na bari na tafi Umu’ahiya a Jihar Abiya,” inji shi.
‘Na taba yin shekara 10 ban ga dan Arewa ba’
Baba Iwuru wanda ya ce a karshe ya koma aikin gadi, Aminiya ta gano a yanzu ba ya da wata sana’a a yanzu saboda karfi ya qare masa, kuma babu wani abin da ya ajiye ko sututar kirki ba ya da ita.
Ya ce, “Daga nan na sake barin garin Umu’ahiya na taho Kalaba. Ina zaune a can cikin gari na samu aikin gadi. Na shafe sama da shekara goma ban taba ganin wani dan uwana mutumin Arewa ba, sai da wani daga cikin makwabtanmu ya ce da ni Baba akwai fa ’yan uwanka Hausawa a garin nan, wata rana zan kai ka, ka gan su. Na ce masa to.
“Ranar Juma’a kuwa ya kawo ni, na yi Sallah na ga mutanenmu, sai dai babu wani idon sani. Haka ya mayar da ni, kowace Juma’a ana kawo ni in yi Sallah a mayar da ni gidan da nake aiki.”
Da wakilinmu ya tambayi Najume Garba ko yaya yake yin jinya idan ya kamu da rashin lafiya? Sai ya ce “Gidan da nake aiki ne suke kai ni asibiti. Daga baya kuma da na bar aiki saboda an mayar da maigidana wani wuri, sai na koma Iwuru da zama can ma babu wata sana’a da nake yi face gadi,” inji shi.
Najume ya ce wata rana yana zaune a kauyen Iwuru, sai suka hadu da wani dan garinsu, hakan ne ya sa bayan sun rabu, sai ya bar garin ya koma kauyen Akampa don kada ma ya kai labarinsa a zo nemansa.
Najume, ya ce yanzu dai karfi ya kare aikin gadi ba ya samuwa gare shi, kuma ko ya yi niyyar komawa gida Arewa can ban ajiye ba bai kuma ba wani ajiya ba, don haka ba ya tsammanin ma idan ya koma zai iya gane gidansu bare abokai.
“Ka san mutumin karkara idan ka watsar da shi, shi ma haka zai watsar da kai, tunda ba iyali ne da ni ba a nan, haka zan ci gaba da zama har rayuwar ta karasa tunda dan zancen nan da muke yi ban mallaki koda Naira dubu daya ba, a nan Iwuru kowa ya zo ni ya tarar inda mutanen suke ba ni ci da sha su ce Baba ga abinci,” inji Najume.
A birnin Ibadan da ke Kudu maso yamma kuwa shugabannin al’ummar Hausawa ne suka raba auren wani Bahaushe da matarsa Bahaushiya saboda ya ki fada mata sunan gari ko kauyen da ya fito.
Ma’auratan wadanda aka sakaye sunansu wata majiya ta kusa da matar ta ce, “Yanzu hakan wannan mutum yana da kimanin shekara 65, kum ya je Ibadan ne tun yana dan kimanin shekara 30.
Bayan shekara 10 yana kame-kamen aikin dogaro da kai daga baya sai ya nemi auren wannan mata da suka daidaita aka daura musu aure. Tun daga wancan lokaci matar ta rika damunsa ya kai ta garinsu amma har zuwa lokacin da aka raba aurensu bai kai ta ba bayan shekara 20 suna zaman aure.
Kuma bai taba ko yunkurin zuwa gida domin ganin danginsa ba, kuma ba a taba ganin wani dan uwansa ya zo daga garinsu ba.”
Majiyar ta ce, “A lokacin da mutumin ya isa Ibadan yana da ilimin addinin Musulunci daidai gwargwado amma duk kokarin da muka yi wajen hada shi da malamai suna yi masa wa’azi da nasiha a kan ya fada musu sunan gari ko kauyensu hakan ya ci tura.
“Mun shaida masa idan ma wani laifi ne ya koro shi daga garinsu, to za mu dauki nauyin aikawa da wakilai domin bincikar lamarin ta yadda za a shawo kan matsalar amma ya ki. Wannan ya sa matar ta yi yaji daga gidansa, kuma bayan ta shafe shekara uku tana kai karar neman a raba aurensu a karshe shugabanni sun raba auren. Dangin matar ne suka dauki alhakin kula da rayuwar ’ya’ya biyu da suka haifa.”
Binciken da Aminiya ta gudanar ta gano cewa bayan shekara biyar da kashe auren, har yanzu mutumin bai sake yin wani auren ba, yayin da tsohuwar matar tasa ta sake yin aure.
Wani mutum mai suna Dan’auta (ba sunansa na asali ba ne) mai kimanin shekara 60 Aminiya ta samu labarin cewa shi ma tunda ya je Ibadan bai taba fada wa kowa sunan garin da ya fito ba, amma an tabbatar da cewa ya fito ne daga Arewa maso Yamma.
Shi ma Dan’auta ya auri wata mata inda suka haifi ’ya’ya bakwai a wata unguwa a cikin birnin Ibadan.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya cewa yau shekaru 25 ke nan da Dan’auta ya auri matar, kuma har yanzu suna tare domin matar ba ta taba nuna damuwarta a kan rashin sanin garin mijinta ba.
Dan’auta yana da sana’a har ya taba mallakar motar da ake yi masa dakon kaya zuwa Arewa. “Matsalar da ke tsakaninmu da wannan mutum Dan’auta ita ce kin gaya mana sunan gari ko kauyen da ya fito,” inji wata majiya.
Amma wani dan dako mai suna Malam Dandako mai kimanin shekara 55 lamarinsa ya yi daban domin ya shigo birnin Ibadan da kuruciya ne, kuma saboda kyan halayensa sai mutanen da yake aiki a karkashinsu suka yanke shawarar daukar nauyin komawa da shi garinsu bayan shafe shekara 30 bai je gida ba kuma babu wani dan uwansa da ya zo daga garinsu.
Aminiya ta gano cewa an yi nasarar komawa da Malam Dandako zuwa garinsu na asali a inda ya yi zaman wata biyu da danginsa a garinsu a Arewa, kafin ya dawo Ibadan ya ci gaba da aikin dakon da ya saba tare da auren matar da suke zaune da ita a yanzu.
Malam Dandako ya shaida wa Aminiya cewa “Ni dai ban yi wani laifi da ya koro ni daga garinmu ba, sai dai Shaidan ne ya sa na shafe shekara 30 ban koma gida ba. A lokacin da na isa garinmu na asali na tarar mahaifina da mahaifiyata sun koma ga Allah, amma sauran dangi sun yi matukar farin ciki da ganina kuma yanzu haka suna kawo min ziyara lokaci-lokaci, ni ina zuwa ganin gida a kowace shekara.”
Bincike ya nuna cewa akwai maza da mata masu yawa da suke fitowa daga garuruwansu zuwa wasu garuruwa da sunan yawon duniya. A yayin da wadansu suke fitowa a dalilin aikata wani abin kunya a garinsu na asali, wadansu kuwa ana zargin asiri ake yi musu a raba su da kauyuka da garuruwansu na asali.