Daruruwan Hausawa mazauna Jihar Oyo na kaura zuwa Arewa bayan rikicin da ya barke a yanin Sasa da ke Ibadan wanda ya yi sanadiyar asarar rayuwa da dukiyoyi.
Aminiya ta gano cewa baya ga wadandan suka koma Jihohin Kano, Sakkwato, Kebbi, Kaduna, Jigawa da sauransu, kimanin mutun 500 ke zaman mafaka a Babbar Tashar Mota ta Akinyele a garin Ibadan.
- ‘2023: Arewa za mu sake ba takarar Shugaban Kasa a PDP’
- Rikicin Hausawa da Yarbawa: Fusatattun matasa sun hana gwamnoni shiga fadar Sarki
- Yadda Okonjo-Iweala ta zama sabuwar shugabar WTO
Da yake tabbatar wa Aminiya cewa mutanen Arewa na ta komawa gida, Magajin Garin Hausawan Ibadan, Alhaji Usman Garba, ya ce, “Ba wata hukumar agajin gwamnati ko kungiya mai zaman kanta da da kawo mana dauki ko kayan agaji.
“Mutanenmu na shiga tireloli da bas-bas suna komawa Arewa. Ba wanda sa ce musu su koma Arewa sai saboda yawancinsu sun yi asarar duk abin da suka mallaka a rikicin.”
Shugaban tashar motocin, Alhaji Yaro Abubakar, ya shaida wa wakilinmu cewa tun ranar Juma’a matasan ke zaune a garejin bayan yawancinsu sun tako daga Kasuwar Sasa da wasu unguwannin da ke makwabtaka da ita.
Wasu Hausawan da suka bar Sasa ranar Juma’a zuwa Asabar sun ce sun ba jami’an tsaro N5,000 zuwa 10,000 don su yi musu rakiya zuwa inda za su samu tsira a gidan Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin da wasu wurare.
Wani daga cikinsu ya shaida wa Aminiya cewa sun ba da kudaden ne saboda su samu a isar da su inda za su samu tsira ba tare da an kashe su ba.
Rikicin ya barke tsakanin al’ummar Hausawa mazauna da Yarabawa ’yan kasa a Kasuwar Sasa inda aka ba wa hamata iska a Kasuwar daga ranar Alhamis 11 zuwa Juma’a 12 ga Fabrairu, 2021.
Rikicin wanda ya samo asali tsakanin wata mata Bayarabiya da wani dan dako dan Arewa ya yi sanadin mutuwar kimanin mutum 30 tare da kona kantuna da gidaje da kuma motoci a bangarorin biyu.
Rahotanni sun nuna cewa daga baya an girke jami’in staro kuma kura ta lafa a yankin Sasa da makwabtanta.
Amma shugabannin ’yan Arewa da wasu da aka raba da muhallansa sun shaida wa Aminiya cewa wancinsu da suka hada da mata da kananan yara na ta komawa Arewa.
Wasu da abin ya shafa sun ce dole su bar Ibadan saboda sun rasa duk abin da suka mallaka na gidaje da shaguna sannan babu wani tallafi da suka samu daga Gwamnatin Jihar Oyo ko ta Tarayya.
Halin da ’yan Arewa suka shiga
Shugaban tashar motocin, Alhaji Yaro Abubakar, ya ce Shugaban Matasan Hausawan Ibadan, Alhaji Nasiru Muhammad Naharande tare da taimakon wasu attajirai ne sauka dauki nauyin ba wa masu gudun hijirar da ke zaune a tashar motar abinci sau uku a kullum.
Yawancin mutanen da muka zanta da su sun ce ba za su koma Kasuwar Sasa ba har sai gwamnati ta dauki kwakkwaran matakin tabbatar da kare rayukansu da dukiyoyinsu.
Yanayin tsaro
Game da yanayin tsaro a Sasa, ya saida wa wakilinmu cewa, “Abin ya burge mutanenmu saboda yadda aka girke jami’an ’yan sanda da DSS, da sojoji da NSCDC da Amotekun a nan; suna da lura tare da bincikar masu shiga ko fita daga Sasa.”
Kula da masu hijira
Game da kula da abinci da suran bukatun masu hijirar, Alhaji Garba ya ce, “Mun mayar da wasunsu Sabo a Mokola domin rage nauyin da ke kan Sarkin Sasa.
“Mu ma muna hada kudi muna tallafa wa mutanen da abinci.
“Da na je Sasa sai da na zubar da hawaye. An kashe mutane da dama amma ba a bayar da rahoto ba.
“’Ya’yanmu ba su da wurin kwana, wasu na fama da yunwa. Tun daga ranar, mu ke yin karo-karo domin mu ciyar da su.
“Yanzu na kira kanina ya fito da ragowar buhun shinkafar da ta rage a gidanmu a kai wa mutanen da suka rage a gidan Sarkin Hausawa,” inji shi.