Yajin aikin da masu baburan A Daidaita Sahu suka fara a Jihar Yobe ya kawo tsaiko ga harkokin sufuri da kasuwanci, inda masu shaguna suka rufe saboda gudun tashin hankali.
Aminiya ta ruwaito cewa mambobin kungiyar masu haya da baburan na A Daidaita Sahu na yajin aikin ne kan zargin jami’an hukumar kula da Sufuri na jihar (YOROTA) da addabar su musamman ta hanyar kama su tare da yi musu tara haka siddan, wanda suke ganin keta musu haddi ne.
Wannan tataburza da yajin aikin ya jawo matasa na yawo kan hanyoyin tsakiyar garin , almarin ya sa ’yan sanda bin su suna jefa musu barkonon tsohuwar tare da tarwatsa su, don gudun tashin wata tarzoma.
A gefe guda kuma, ma’aikata da sauran al’umma sun kamo yin tattaki da kafa don zuwa wuraren aikin su da sauran bukatu, a safiyar Talata a Damaturu, babban birnin jihar.
- Albashin sojan Nijeriya N50,000 ne —Babban Hafsan Tsaro
- Bolaji Agbede ta zama shugabar riko na Bankin Access
Duk kokarin Aminiya na jin ta bakin shugaban kungiyar ta masu haya da baburan, Alhaji Umar Barau, kan lamarin ya ci tira, kuma wayarsa na shiga amma ba ya dauka.
Haka nan shi ma shugaban hukumar ta YOROTA na jihar, Alhaji Babagana Alhaji Mofu (Bature Goneri) shi ma lamarin haka yake.
Sai dai wata majiyar na bayyana cewar dukanin bamgarorin na can na gudanar da taruka don gano bakin zaren wannan lamari.