Wayar salula ka iya yada cutar coronvirus, musamman idan ba a yawan wanke hannaye da kuma goge jikin wayar bayan an yi amfani da ita, inji masana.
Masanan sun kuma jaddada muhimmancin tsafta wajen dakile yaduwar annobar coronavirus.
Daya daga cikinsu, Amos Ezekiel, wanda masanin cututtuka a Asibitin Koyarwa na Barau da ke Kaduna, ya ce shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) cewa mutane kan manta cewa kwayar cutar coronavirus kan makale a jikin wayoyin salula.
“Abu muhimmi shi ne a tsaftace duk inda hannaye ke tabawa kamar hannun kofa, da duk wasu wurare da dan-Adam yake yawan tabawa kamar wayar tarho.”
- An kashe mutum 15 a Taraba —’Yan sanda
- Gaskiyar lamari game da fasahar sadarwa ta 5G
- COVID-19: A yi biyayya ga gwamnati —Masana
Ya kuma ce mutum ka iya tsaftace hannunshi a kai a kai, amma kwayoyin cutar da ke makale a jikin wayar salularshi irin su coronavirus ka iya koma hannun.
“Abu ne mai matukar sauki ka dauki kwayoyin cuta da tsaftataccen hannunka ta hanyar taba abin da mai dauke da su ya taba.
“A lokaci irin wannan da ake fargabar yada cutar coronavirus, akwai bukatar a yi amfani da man tsaftace hannu, wato sanitizer a goge wayar hannu.
“Za a iya samun auduga a diga man tsaftace hannun a goge duk jikin wayar salular”, inji shi.
Ezekiel ya kuma ce akwai bukatar jama’a su guji yin amfani da wayar da ba tasu ba, musamman idan mai wayar na da lalurar da ta shafi numfashi ko alamunta suka yi kama da mura.