✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mai kiran matarsa sama da sau 100 a rana ta wayar salula

Ina son matata, kuma ina yin waya da ita ba tare da na ce komai ba.

A ranar 10 ga Yuli, wata mata mai shekara 31 daga Amagasaki, a lardin Hyogo na Japan, ta fara samun kiraye-kirayen waya daga wani wanda zai yi shiru kawai har sai ta katse cikin takaici.

Wannan ya ci gaba har tsawon makonni, saboda kiran na shigowa ne daga lambar wayar da ba a san ta ba, don haka matar ba za ta iya rufe layin kiran ba.

A galibin ranaku tana samun kiraye-kirayen waya, amma wani lokaci, wayar kan rika karar alamar kira sama da sau 100 a rana.

An yi sa’a, wayar ba ta taba yin kara a cikin dare ko lokacin da take kallon bidiyo a wayar mijinta ba, wanda a karshe ya sa ta tunanin wane ne wannan mai kiran ta haka.

Ya yi ta kiran a watan Yuli ya koma Agusta kuma ana ci gaba da kiran wayar, wanda daga karshe ta yanke ta fara tunanin yadda za ta tona asirin mai kiran ta.

Da zarar ta nazarci yanayin kiran, sai ta fara zargin mijinta.

Lokacin da ba ta taba samun wani kira mai ban haushi ba shi ne da daddare lokacin da suke tare da kuma lokacin da take yin amfani da wayarsa don kallon bidiyo.

A karshe, matar ta tuntubi ’yan sanda don taimaka mata su gano mata dalilin kiran, tare da bayyana musu tunaninta na cewa mijinta zai iya zama mai yawan kiran nata.

Bayan gudanar da bincike, jami’ai sun tabbatar da zargin matar, kuma a ranar 4 ga Satumba, an kama mijinta a Amagasaki bisa karya dokar Japan ta kiran waya da lambar da a san ta ba.

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa yake yi wa matarsa haka fiye da wata guda tare da kira da bakuwar lamba, sai kawai mutumin ya amsa da cewa, “Ina son matata, kuma ina yin waya da ita ba tare da na ce komai ba, kamar dai yin shirun da nake yi ya nuna cewa ina son ta.”

Ba sabon abu ba ne ma’auratan da ke Japan su kasance a wuri daban-daban, musamman saboda yanayin aik.

Sai dai ’yan sanda a Amagasaki sun tabbatar da cewa wannan shi ne karo na farko da aka samu wasu ma’auratan da suke zaune tare, amma daya na kiran wayar tarho da bakuwar lamba.