✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda wata matashiya ta maka mahaifinta a kotun Musulunci

Matashiyar tana zargin mahaifinta da kin aurar da ita ga saurayin da take so

An samu tsaiko a sauraron karar da wata matashiya mai suna Halima Yunusa ta kai wata kotun Musulunci tana zargin mahaifinta da kin amince mata ta auri wani saurayi mai suna Bashir Yusuf.

Wani korafi da mahaifin saurayin, Malam Muhammad Yusuf, ya shigar ne a gaban Kotun Daukaka Kara ta Shari`ar Musulinci ya haddasa lamarin.

A ranar 16 ga watan Mayu kotun, mai zama a Magajin Gari da ke Kaduna, ta bukaci Malam Muhammad ya bayyana a gabanta domin amincewa dansa Bashir ya auri matashiyar.

Sai dai kuma ko da ya amsa kiran kotun a zamanta na karshe, sai ya shigar da korafi a rubuce, lamarin da ya yi sanadiyar tsayawar shari`ar.

Alkalin kotun, Mai Shari`a Murtala Nasir, ya nuna mamakinsa, tare da cewa yana kokarin yin dukkan mai yiwuwa don ganin Malam Muhammad ya bar dansa ya auri Halima.

Daga nan sai ya dage zaman shari`ar ba tare da sanya ranar cigaba ba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya {NAN} ya ruwaito cewa  a zaman kotun na karshe, alkali ya shawarci Malam Muhammad da ya bari masoyan su auri juna, domin idan ya ki kotun za ta shiga gaba ta aurar da su ko ba amincewarsa.