✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda wata mata ta kona kanwarta

Tun lokacin da mahaifiyar yarinyar ta rasu 'ya'yan kishiya ke ta azabtar da ita.

‘Yan sanda sun damke wata mata da ta watsa wa diyar kishiyar mahaifiyarta tafasasshen ruwa.

Kwamishinar Mata ta jihar Kogi, Hajiya Fatima Kabir Buba, ta ce bayan samun labarin abun matar ta yi wa yarinyar ‘yar shekara 14 ne suka sanar da yan sanda kafin aka kama mai laifin.

Da take bayani, kwamishinar ta ce, yarinyar ta rasa mahaifiyarta a shekarun baya, kuma tun daga sannan ‘ya’yan kishiyar uwarta suke gallaza mata.

Ta ce, ruwan zafin ya kona yarinyar a sassan daban daban na jikinta amma gwamanti ta dauki nauyin yi mata magani.

Haka kuma Kwamishinar takwatanta abun da aka yi wa yarinyar da rashin tausayi da zalunci.

Ta kuma sha alwashin ci gaba da tsaya wa yarinyar har sai an bi mata kadinta.