✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda wata gobara ta gagari motocin kwana-kwana uku a Abuja

A Yammacin ranar Juma’a ce wata gobara ta lakume wani katafaren gida a Unguwar Jabi da ke cikin Babban Birnin Tarayya Abuja. Bayan tashin goborar…

A Yammacin ranar Juma’a ce wata gobara ta lakume wani katafaren gida a Unguwar Jabi da ke cikin Babban Birnin Tarayya Abuja.

Bayan tashin goborar da misalin karfe shida wakilinmu da ya ziyarci inda iftila’in ya auku ya zanta da wasu makwatan gidan, inda suka ce, gidan ba kowa a lokacin da gobarar ta tashi sai a wasu lokutan masu gidan na zuwa su kwana a ciki.

Wani da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce, bayan gobarar ta tashi zuwa wani dan lokaci sai motar kashe gobara ta Birnin Tarayya ta kawo dauki gidan.

Wakilinmu ya samu motar kashe gobarar amma ba ta dade ba da fara kokarin kashe wutar ba kwatankwacin minti 20, ruwan kashe gobarar ya kare.

Daga bisani wata motar kashe gobarar biyu ta kawo nata daukin amma ita ma ba ta dade ba, ta gaza kashe wutar yayin da gobarar ke ci gaba mamaye gidan kamar ana kara mata makamashi.

Zuwa wani dan lokaci sai motar kashe gobara ta zo a sukwane, hakan ne ya sa aka ci karfin gobarar wadda ta riga da lakume komai na gidan musamman saman benen.

Ga hotunan yadda aka rika dauki ba dadi da gobarar: