✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda wanda ya sayar da ’ya’yanmu ya yaudare mu da batun makaranta — Sakkwatawa

A ranar Larabar makon jiya ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato a karkashin jagorancin Kwaminshinanta Malam Hayatu Kaigama ta gabatar da wani magidanci mai suna…

A ranar Larabar makon jiya ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato a karkashin jagorancin Kwaminshinanta Malam Hayatu Kaigama ta gabatar da wani magidanci mai suna Bala Abubakar bisa zarginsa da sayar da kananan yara 28 ciki har da ’ya’yansa shida a lokuta daban-daban.

Kama wanda ake zargin ya biyo bayan ci gaba da bincike ne da ’yan sanda ke yi game da kama wata ’yar sanda mai suna Kulu Dogondaji da wata mace mai suna Elezabeth Ojah tare da yara biyar da aka yi a Abuja a watan jiya kamar yadda Aminiya ta bayar da labarin.

A binciken da Aminiya ta gudanar ta gano cewa Bala Abubakar wanda ba ta samu takamaimiyar sana’a ko aikin da yake yi ba, illa wata majiya ta shaida mata cewa yana bugebuge ne, yana da mata uku, biyu suna zaune a gida daya, sai dayar da take zaune daban, kuma dukkan gidajen biyu haya yake yi a cikinsu.

Ya riƙa tara mata yana ba su tallafin kuɗi — Makwabta

Sai dai kokarin wakilinmu na jin ta bakin matan ya ci tura, saboda sun ki yin magana da shi bisa dalilin mijinsu bai ba su damar yin magana da manema labarai ba.

Amma wani daga cikin makwabtansa da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce bai yi mamakin kama Bala da wannan harkalla ba, domin ya dade yana mu’amala da mata, inda yake tara mata da yawa a unguwar da sunan zai ba su taimako yana yaudararsu da kuɗi.

“Bala mutum ne mai kwadayi da sa kansa inda bai kai ba, don haka babu mamaki komai aka ce ya shiga.

“Tun lokacin da ya dauko harkallar nan muka san dole wani lokaci asiri zai tonu, yana yaudarar mata da kudi kamar Naira dubu 50, da fada masu za a kai yaransu karatu, su kuma saboda son banza sai suka rika aminta da haka,” in ji shi.

Kan zargin sayar da ’ya’yansa ya ce “Haka ne ya mika ’ya’yansa amma muna kallon hakan salo ne na yaudara domin mutane su gamsu cewa shi da kansa ya bayar da nasa in da cuta ce ba karatu ba, bai zai yi haka ba, a haka ya yi ta yaudararsu suna mika ’ya’yansu.”

“Tun lokacin da na ga Bala yana auri-saki har ya auri mata biyar inda yake zaune da uku na sallama cewa komai zai iya yi, shi kadai ya san yawan ’ya’yansa.

“Da na samu labarin kama shi ban yi mamaki ba, akwai mutanen da ba ya magana da su, saboda suna zargin yanayin rayuwarsa,” in ji shi.

‘Matarsa ta taɓa tayar da liƙi ya dawo da ɗanta’

Wata makwabciyarsa ta ce bai wuce shekara biyar a yankin nasu ba, da farko sun dauke shi mutumin kirki da ke son taimakon marasa karfi, daga baya suka fahimci ba haka ba ne yaudara ce ta shi, sai suka sa masa ido.

“Mun nesanta kanmu da iyalansa tun lokacin da labari ya fito cewa ya sayar da ’ya’yansa uku. Da matarsa daya ta kunna wuta kan ya dawo mata da danta ko ta tona masa asiri, sai ya dawo da shi, sai ga wannan ta bulla, ban yi mamakin kama shi ba,” in ji ta.

Wani makwabcin ya ce, “Duk wanda zai gaya maka gaskiyar halin Bala ba mai dadi zai gaya maka ba, domin kowa ya san shi a unguwar nan yana tara mata da sunan za a samar musu tallafi su da ’ya’yansu, ya rika karbar kudinsu.

“Mu saboda ba hukuma ba ce muka sa masa ido, wani lokacin yana amfani da siyasa ya je ya samo tallafin kudi ko sutura ya raba wa mata da yara, hakan ya sa ya kara samun karbuwa ga matan.

“Duk abin da ya kawo suna yarda, na yi yakinin wani lokaci sai ya shiga komar hukuma kan wannan yaudara, yanzu a lungu daya fa an ce yara 17 aka ba shi, wane irin rashin hankali ne wannan?”

Habiba Abubakar mai shekara 40 tana cikin mahaifan da suka bayar da ’ya’yansu amma ta ce ba sayarwa ta yi ba, yaudararsu aka yi.

“Dana Muzakkir Kabir mai shekara 7, Bala ya samu surukata cewa akwai wata makaranta da aka fito da ita ta haddar Kur’ani da yake son ta bayar da jikanta a kai, komi za a yi masa amma yaran zai rika tahowa ganin gida in an yi hutu.

“Da ya gamsar da uwar mijina ne ta ce a bayar da shi ni da mahaifina ba mu so ba, amma gudun fushinta muka bari, bayan tafiya da shi hankalina bai kwanta ba.

“A nan ne na bukaci ganin dana, tunda an ce makarantar a nan Sakkwato ake karatun, a kokarinsa na kwantar da hankalinmu ya fada mana ai ya kai ’ya’yansa 4 da na yayansa biyu, da an yi hutu yaran za su dawo.

“Muna cikin wannan ne sai asiri ya tonu, ’yan sanda suka gano dana yana Enugu, matar da ta sayi dana ana ce mata Anti Sarah tana Ingila,” in ji ta.

Ta ce abin da suka samu labari ta sayi dansu ne daga hannun su Bala a kan Naira miliyan 3, mu dai ’yan sanda sun tabbatar mana sai an dawo mana da danmu tunda an gano garin da yake.

Wata da ta bai wa Bala jaririya mai mako uku da haihuwa da yara uku mata masu shekara 6 da 9 da 10, ta ce ta fi shekara 20 tana hulda Bala a harkokin taimakon marayu ba ta san ya sauya zuwa wannan harka ta yaudara ba.

“Bala ya same ni ya ce min akwai wata makaranta da aka bude ta yara da za a ba su ilimi kyauta duk bayan wata uku za a dawo da yaran su ga gida su koma.

“Muka yi da shi duk mako uku za mu tafi mu ga yaran a inda suke ya yarda. A haka na ba shi yaran, da lokaci ya cika muka rika bin sa amma yau da gobe kawai yake mana har yaran nan suka yi wata shida a hannunsa.

“Sai ga asiri ya tonu an kama su a Abuja, mu har an kai yaranmu kauyen Jos an mayar da su Kirist an canja masu suna, ’yan sanda sun yi kokari sosai,” in ji ta.

Ta ce sun samu labarin ana sayar da yaran ne farashi dabandaban wasu a Naira miliyan biyar wasu miliyan uku wasu dubu 150 ya danganta da yaro.

“An yaudare mu kan zaman amincin da muke yi da shi kan harkokin marayu da ake yi a tsakanin Hukumar Zakkah da Wakafi,” in ji ta.

Kan yadda aka yi ta ba shi jinjirar mako uku, sai ta ce wata diyyarsu ce ta haife ta ba da aure ba, kula da yarinyar na yi mata wahala, shi ne ya ce a bayar da ita domin a kula da ita suka ga hakan zai fiye wa yarinyar da wannan wahalar ashe tunaninsa daban.

Hakimin Tudun Wada, Malam Sanusi Mai Unguwa ya ki yin magana a kan batun, ya ce sai Yariman Tudun Wada ya ba shi umarni duk da wakilinmu ya samu Yarima ya bayar da umarnin an kasa samun hakimin.

Mun gano yara ƙarin yara 21 da ya sayar a jihohi uku — ’Yan sanda

Lokacin da Kwamishinan ’Yan sandan ke gabatar da Bala ga manema labarai, Bala ya ce ba sayarwa da yaran ya yi ba hasali taimako rayuwarsu yake son yi.

Kwamishinan ya ce mata biyu da suka tafi da yaran tare da jinjirar mako biyu zuwa Abuja sun tabbatar wa ’yan sanda ba ’ya’yansu ba ne, amma da yarda iyayensu suka karbo su don aika wa wata kungiya ta sa-kai domin su kula da yaran har su yi karatu bayan sun girma a dawo wa iyayensu da su.

Kwamishinan ya ce, “Wannan jawabi bai gamsar da mu ba, akwai lauje cikin nadi, hakan ya sa aka kira mu muka tafi Abuja muka tarar da matan biyu da yara biyar da suka tafi da su.

“A haka Allah Ya taimaka aka samu iyayen yaran suka tabbatar an yaudare su ne aka tafi da yaran da sunan za a sa su makaranta, bayan sun yi karatu a dawo da su, ganin sauki ya samu daga cikinsu zawarawa ne kula da yaran na wahalar da su, sai suka amince.

“A binciken da muka fadada sai muka gano akwai jihohi uku da aka kai yaran aka boye, da muka ci gaba da bincike muka ceto yara ’yan asalin Jihar Sakkwato 21, bayan biyar na farko sai suka zama 26, cikin ikon Allah mun dawo da dukkan yara 21,” in ji Kwamishinan ’Yan sandan.

Kwamishina Ali Kaigama ya kara da cewa Bala Abubakar da ke zaune a Unguwar Tudun Wada a Karamar Hukumar Sakkwato ta Kudu a Jihar Sakkwato ya sayar da hatta ’ya’yansa su shida bayan hada baki da aka yi da shi yana kawo yara ga Kulu Dogonyaro da Elizabeth Ojah ana biyansa Naira dubu 150 zuwa Naira dubu 250.

Ya ce wanda ake zagin ya sayar da yara 28 ne kafin dubunsu ta cika shi da abokan huldarsa. Sai dai Bala Abubakar ya shaida wa Aminiya a hedikwatar ’yan sandan cewa ba sayar da yaran ya yi ba, bayanin da Kulu ta yi masa ne ya gamsu cewa harka ce ta taimakon yara su samu karatu.

“Wanda ya hada ni da ita sai da na yi masa magana cewa kada ya yi abin da zai jawo min rigima domin ina cikin mutane, ya tabbatar min ba matsala, mun ba da yara shida kuma kowane an dawo da su hakan ya sa na samu gamsuwa na dauki ’ya’yana na bayar,” in ji shi.

Ya kara da cewa, “A gaskiya na yi da-na-sanin abin da na yi domin abin da na gani a yanzu bai yi min dadi ba, ba zan sake shiga cikin irin wannan lamari ba, ko wa ya kawo shi.”

Ya ce bai taba damuwa kan tura ’ya’yansa da na mutane da ya yi ba domin ya dauka lamari ne mai kyau saboda ya aminta da wadanda yake mika wa yaran don su tafi a kula da su.