Ana zargin wani mahaifi da lakada wa dansa dukan da ya yi ajalinsa saboda zargin satar masa kaya a shagonsa na kasuwanci.
Rundunar ’yan sanda a jihar Kano ce ta tabbatar hakan da kuma kama wanda ake zargin.
Mai magana da yawun Rundunar, DSP Abdullahi Kiyawa, ya ce mamacin mai shekara 19 ya rasu ne bayan mahaifinsa ya lakada masa duka a daren ranar Juma’ar da ta gabata.
Mahaifin nasa ya yi masa dukan ne bisa zargin dan da satar galan biyu na manja a kantinsa.
A ranar Litinin ce matashin ya ce ga garinku yayin da yake jinyar dukan da mahaifin nasa ya yi masa a Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed da ke kwaryar birnin Kano.
Shaidu sun ce suna zaune a shagonsu sai suka ga mahaifin mamacin yana dukan sa.
“Muna zaune a bakin shagonmu, sai muka ji yana duka yaronshi a cikin shago.
“Amma ba mu da masaniya a kan musabbabin duka yaron kuma ganin cewa abu ne tsakanin uba da dansa ya sanya ba mu tanka masa ba.
“Sai daga baya wani makwabcinsa mai wankin hula ya nemi shi ga tsakani amma mahaifin ya daka masa tsawa cewa ya fitar masa daga shago.
“Ganin haka ya sanya muka koma gefe muka zama ’yan kallo,” inji Kabiru.
Ita kuwa mahaifiyar yaron, wacce ta rabu da mahaifinsa tsawon lokaci, ta ce ganin karshe da ta yi wa dan nata shi ne lokacin da ta kai shi asibiti bayan da ya zo gidan mijinta a unguwar Danbare cikin wani mawuyacin hali.
“Kawai sai ganin sa na yi a gefe na a kwance, na ce Abba mai ya same ka, sai cewa ya yi babanmu ne ya dake ni.
“Na ce mai ka yi masa, sai ya ce wai mansa ne bai gani ba guda biyu kuma na rantse masa da Allah ba ni na dauka ba amma ya kama ni da duka.
“Sai na ce yanzu me ke damun ka, sai ya ce kansa ne yake masa ciwo domin a ka ya dake shi,” inji mahaifiyarsa.
DSP Kiyawa ya kara da cewa, mahaifin a yanzu yana hannunsu inda ake ci gaba da gudanar da bincike.
“Yanzu yana hannunmu, kuma Kwamishinan ’Yan sandan Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ya sa a dawo da shi sashen manyan laifuka a nan Hedikwatarmu da ke Bompai.
“Dole sai muna kai zuciyarmu nesa, duk inda aka ce yau ka na tare da wani an samu sabani, a daina kai duka ko da kuwa da hannu ne, saboda ba’a san mai zai faru ba,” in ji DSP Kiyawa.