✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Malawi ya harbe kansa a majalisa

Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin kasar Malawi, Clement Chiwaya, ya hallaka kansa ta hanyar harbi a ka a cikin ginin majalisar. Mai kimanin shekara 50,…

Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin kasar Malawi, Clement Chiwaya, ya hallaka kansa ta hanyar harbi a ka a cikin ginin majalisar.

Mai kimanin shekara 50, dan siyasar ya harbe kan nasa ne ranar Alhamis a cikin majalisar inda ya je don tattauna batun wasu kudaden alawus dinsa na abin hawa, lokacin da ya bar mukaminsa a 2019.

Sai dai Kakakin ’Yan Sandan kasar, James Kadadzera, ya ki ya ce uffan kan batun, inda ya ce dole sai an kammala bincike kafin ya yi tsokaci a kai, kuma ba zai iya tabbatar da faruwar lamarin ba.

A cikin wata sanarwa da majalisar kasar ta fitar ranar Juma’a, ta ce, “Majalisa na bakin cikin sanar da jama’a cewa tsohon Mataimakin Kakakinta ya kashe kansa a cikin gininta.”

Majalisar dai ta alakanta kisan da bacin ran da ya shiga, sakamakon jan kafar da aka yi wajen biyan shi hakkokinsa da kudaden alawus-alawus na ababen hawa.

Clement dai ya sayi sabuwar mota a karshen wa’adinsa a 2019 kamar yadda dokar kasar ta tanada.

Sai dai ya yi ta kokarin ganin majalisa ta amince a biya shi kudin gyaran motar bayan ya yi wani hatsari da ita wata shida bayan sayenta, amma hakansa ya gaza cimma ruwa.