Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin kasar Malawi, Clement Chiwaya, ya hallaka kansa ta hanyar harbi a ka a cikin ginin majalisar.
Mai kimanin shekara 50, dan siyasar ya harbe kan nasa ne ranar Alhamis a cikin majalisar inda ya je don tattauna batun wasu kudaden alawus dinsa na abin hawa, lokacin da ya bar mukaminsa a 2019.
- Babu kasar da ta ci gaba ta amfani da harshen aro Masani
- Trump ya maka Twitter a kotu kan kin bude shafinsa
Sai dai Kakakin ’Yan Sandan kasar, James Kadadzera, ya ki ya ce uffan kan batun, inda ya ce dole sai an kammala bincike kafin ya yi tsokaci a kai, kuma ba zai iya tabbatar da faruwar lamarin ba.
A cikin wata sanarwa da majalisar kasar ta fitar ranar Juma’a, ta ce, “Majalisa na bakin cikin sanar da jama’a cewa tsohon Mataimakin Kakakinta ya kashe kansa a cikin gininta.”
Majalisar dai ta alakanta kisan da bacin ran da ya shiga, sakamakon jan kafar da aka yi wajen biyan shi hakkokinsa da kudaden alawus-alawus na ababen hawa.
Clement dai ya sayi sabuwar mota a karshen wa’adinsa a 2019 kamar yadda dokar kasar ta tanada.
Sai dai ya yi ta kokarin ganin majalisa ta amince a biya shi kudin gyaran motar bayan ya yi wani hatsari da ita wata shida bayan sayenta, amma hakansa ya gaza cimma ruwa.