Hukumomin kasar Saudiyya sun sanar cewa a ranar Talata, 27 ga watan na Yuni ce alhazai da ke Aikin Hajjin bana za su yi tsayuwar Arafat.
Bayan sanar da cewa an ga sabon watan Zhul-Hajj a ranar Lahadi, inda gwamnatin Saudiyya ta ce Babbar Sallah za ta kasance a ranar Laraba 28 ga watan Yuni a kasar.
- ‘Tinubu zai samar da sola don rage wa ’yan Najeriya radadin cire tallafin mai’
- ’Yan Boko Haram sun kashe manoma 15 a Borno
Gwamnatin kasar ta sanar da haka ne bayan ta tabbatar da ganin watan Zhul-Hajj a ranar Lahadi, 18 ga watan na Yuni.
Don haka a ranar alahzai za su yi jifa da kuma hadaya, bayan sun dawo Mina daga Muzdalifa.
Tsayuwar Arafat babban rukuni ne na aikin Hajji, wadda sai an halartarce ta, ibadar ta Hajji take cika.
Alhazai suna yin tsayuwar Arafat ne a ranar 9 ga watan Zhul-Hajj, inda gaba dayansu suke taruwa su wuni suna yin ibada da addu’o’i a filin Arafat.
Gabanin Magaribar ranar za su wuce filin Muzdalifa su kwana, washegari da hantsi kuma za su koma Mina, inda za su yi jifa da aski da kuma yanka dabbarsu ta hadaya.
A ranar 8 ga watan Zhul-Hajj (Ranar Taraiyar) ake fara aikin Hajji, inda a ranar alhazai suke daukar harama, su taru a Mina, kafin washegari su yini a filin Arafat.
A yayin halartar tsayuwar Arafat, alhazai za su yi sallolin Azahar da La’asar a hade kuma kasaru, bayan limami ya gabatar huduba.