Farashin takin zamani a Kano na ci gaba da tashi, lamarin da ya jefa manona a jihar cikin damuwa da kuma tararrabin makomar noman ranin da suke yi, wanda suka ce yana neman fin karfinsu, idan har tsadar ta ci gaba.
Haka kuma, hakan na iya kawo cikas ga kokarin da suke yi na cike gibin karancin abincin da aka samu a jihar a daminar bara.
Binciken Aminiya ya nuna cewa, a yanzu ana sayar da buhun Takin Uriya mai nauyin kilo 50 kan Naira 37,000, yayin da nau’in NPK 10:10 da 15:15 ya kai Naira 23,000 da kuma Naira 25,000, wanda wannan shi ne tashin farashi mafi muni a cewar masana aikin gona.
- Putin ya lashe zaben Rasha karo na biyar
- Yadda Za Ku Samu Sadarwa Da Intanet A Lokacin Da Aka Samu Tangarɗa
Hakazalika, a cewarsu, wani shiri ne da aka yi da gangan domin hana yin noman baki dayansa.
Binciken namu ya gano cewa, tashin farashin bai tsaya a nan ba, ci gaba yake yi, wanda hakan ya kashe wa sauran kananan manoma gwiwar fara noman ranin na wannan shekara kamar yadda suka bayyana wa Aminiya a yayin hira da wasu manoman.
Wani manomi mai suna Malam Habibu Bello Kubarachi ya shaida wa wakilinmu cewa, manona da yawa irin sa sun koma kan dabarun noma na baya don tunkarar wannan kalubale da kuma yadda za su takaita asara.
Ya ce idan sun yi noman, saboda ba za su iya sayen takin ba, don haka ne ma wasaunsu suka yanke shawarar barin harkar noman gaba daya ko kuma neman rancen kudin da za su sayi takin zamani.
“Taki shi ne babbar matsalarmu domin wasunmu tuni sun share gonar da fadinta ya kai sama da hekta 5 domin soma noman, amma takin zamani ya yi tsadar da ba za mu iya saye ba.
“Hakika noman rani a wannan shekarar zai yi wuya, musamman ga kananan manoma wadanda kuma su ne mafi yawa a jihar.
“Tsoronmu shi ne yawancin manoma ba za su yi noma ba da damina soboda hasashen hasarar da muka yi da rani,” inji shi.
Domin samun mafita, Isah Yahaya Gafan, wani manomi a jihar ya shaida wa wakilinmu cewa, sun soma amfani da gishiri da kanwa don maye gurbin Takin Uriya a gonakinsu.
Sai dai ingancinsa bai kai na Uriyan ba a, amma babu yadda za su yi, domin da babu gwara ba dadi.
Kodayake babbar damuwarsu ita ce ta manoman shinkafa da suke shirye-shiryen nomanta da rani. Domin da kyar za su iya yin wani abin a-zo-a gani.
“Manoman shinkafa da ke da burin nomanta a manyan gonakai sun sake shawara saboda karancin takin zamani sakamakonn tsadarsa da kuma karancin abin saye.
“Wannan babban hadari ne, la’akari da yadda ake bukatar shinkafa a kasar nan a matsayin abincin kowa.
“Ya kamata gwamnati ta shigo cikin lamarin nan ko kuma kowa ya shiga halin ni-’yasu’’, in ji shi.
Haka shi ma shugaban Kungiyar Manoma ta Nijeriya (AFAN), Malam Abdulrasheed Magaji Rimingado ya ce, manona ba su taba ganin lokaci mai wuya irin wannan ba, inda ya ce tuni Kungiyar ta yunkura don ganin gwamnati shigo don neman hanyoyin da za ta kawo wa dauki ga manoman.
Kokarin da kungiyar take yi shi ne na yadda gwamnati mai ci za ta farfado da tallafin da a baya suke mora daga gare ta.
“Mun soma tattaunawa da hukumomin jihar kan hanyoyin da za a bullo da su na bayar da tallafi ko kuma farfado da wanda muke cin gajiayarsa a baya da aka yi watsi da shi na shekara da shekaru.
“Muna fatan kwalliya za ta biya kudin sabulu daga tattaunawar da muke yi. Babu shakka rashin samun nasarar hakan zai yi mummunan tasiri kan shirin samar da abinci a wannan jiha da kuma kasa baki daya”.