✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Trust Dialogue na bana ya wakana

A jiya Alhamis ce aka gudanar da taron tattaunawa na Trust Dialogue na bana kuma karo na 16 da Kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily…

A jiya Alhamis ce aka gudanar da taron tattaunawa na Trust Dialogue na bana kuma karo na 16 da Kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya ke shiryawa.

Taron ya wakana ne a dakin taron na Rundunar Sojojin Saman Najeriya da ke Kado, Abuja, inda Farfesa Jibrin Ibrahim ya shugabanci taro, sannan Mai martaba Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III ya kasance babban bako na musamman.

Taken taron na bana mai shi ne: “Matasa a Dimokuradiyya: Matsalolin da Najeriya ke fuskanta.

Da yake jawabi a wajen taron, Farfesa Jibrin Ibrahim ya bayyana yadda siyasar uban gida ke jawo matsala ga ci gaban kasar nan, “Me muke amfani da shi a Najeriya wajen zaben wanda zai gaji mai mulki idan ya kammala wa’adinsa? Kawai dai abin da ake bukata shi ne ka kasance mai ladabi da biyayya ga ubangidanka wanda watakila shi ne Gwamna. Idan har kana yi masa ladabi, to shi ke nan ka cancanta,” inji Farfesa Jibrin Ibrahim.

Daga cikin masu jawabi a taron akwai wanda ya nemi takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar PDP, Sanata Datti Baba-Ahmed, wanda ya yi tabo matsalolin da matasa suke fuskanta a dimokuradiyya, a kasidarsa mai taken: “Taimakon Matasan Su Gane Gaskiya.”

Datti Baba-Ahmed ya ce, “Babban abin takaici shi ne yadda matasan suke kallon abin da ke wakana a gurgunce. Dukan abin da ke jawo matsala a tsarin gwamnati, yana jawo matsala a dimokuradiyya. Wannan ne ya sa ake dakile matasa a tauye musu hakki. Sayen kuri’a shi ma yana kawo wa dimokuradiyya matsala. Ana kallon masu sayen kuri’un ne a matsayin mugaye ba tare da an lura da wadanda suke sayarwa ba. Da yawa daga cikin wadanda suke sayar da kuri’a ana tilasta musu yin haka ne.”

A jawabin, Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Tallafa wa Mutane Maryam Uwais ta ce, “Matasan Najeriya suna kara yawa. Dole mu tabbatar da cewa ba wai mun sa su a cikin siyasa ba kawai, har ma da tabbatar da cewa ana sauraronsu. Matasa ba su da ta cewa a kan harkokin siyasa a kasar nan, yawanci suna dogaro da inda masu gidansu suka dosa ne. A shirye suke su tayar da kayar-baya, sannan su jawo matsalar da su kansu ba sa son shiga,” inji ta.

A jawabin, Shugaban Fafutikar Tabbatar da Sanya Matasa a Harkokin Siyasa  (Not Too Young to Run’ Samson Itodo ya ce a wasu lokutan ma matasan da ake sanyawa su lura da zabe, ko kidayar kuri’a ba su iya ba.

“Ya kamata manyan ’yan siyasa su taimaka wajen koyar da kanana. Mu san wadanda suke yin siyasa ta gaskiya, kuma irin wadannan mutanen ne muke so su koyar da mu,” inji Itodo

 

…’Yan makaranta daga Kenya sun lashe kyautar Naira miliyan 9 na Gwarazan Afirka na Daliy Trust na bana

A shekaranjiya kuma aka karrama Gwarazan Afirka na bana na Daily Trust, inda wadansu dalibai daga kasar Kenya suka lashe kyautar Dala dubu 25.

Daliban su ne Stacy Owino da Purity Achieng da Iby Akinyi da Synthia Otieno da Macrine Atieno a karkashin Kungiyar “The Resotorers” daga birnin Kisumu na Kudancin Kenya.

Wadannan daliban sun lashe wannan babbar kyauta ce saboda yadda suka kirkiri wata manhajar wayar salula mai suna “I-cut” wadda ake amfani da ita wajen yaki da yi wa mata kaciya.

Ita manhajar ta I-cut tana taimakawa ce wajen sanar da hukumomin ceto ko bayar da agaji a duk lokacin da ake shirin yi wa wata kaciya.