✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ta kaya a wasannin Bundesliga

Bundesliga ta fara daukar hankali bayan an yawaita zura kwallaye a wasannin mako na biyu tun bayan dawowar gasar. Yayin da wasu kungiyoyin ke samun…

Bundesliga ta fara daukar hankali bayan an yawaita zura kwallaye a wasannin mako na biyu tun bayan dawowar gasar.

Yayin da wasu kungiyoyin ke samun koma baya, ita kuma Bayern Munich na ci gaba da jan zarenta.

—Bayern Munich na jan zarenta

Tun bayan dawowar wasanni a gasar Bundesliga Bayern Munich ta ci gaba da jan zarenta inda kawo yanzu ta lashe dukkanin wasanninta.

Hakan ya hada nasarar da wadda ta samu a kan abokiyar adawarta Burossia Dortmund da yi wa ci daya mai ban haushi.

Kwallon da dan wasan bayan Bayern Joshua Kimmich ya ci ana minti 43 da fara wasan ne ya ba kungiyar nasara har aka tashi wasan.

Dortmund ta yi azamar kai hare-haren farkewa amma abin ya gagara. Hakan dai ya sa Burossia Dortmund za ta ci gaba da zama ta biyu a teburin Bundesliga da maki 57 a bayan Bayern Munich din mai maki 64.

—Wolfsburg ta ba wa Leverkusen mamaki

Kungiyar Bayern Leverkusen ta sha mamaki kuma ta karbi kwallaye hudu daga hannun kungiyar Wolfsburg wadda ta kai mata ziyara kuma ta yi mata ci 4-1.

A wasan da aka buga a filin wasa na BayArena, sai da wolfsburg ta ci kwallaye hudu kafin Leverkusen ta farke guda daya ana saura minti 85 a tashi wasan.

Wannan sakamako ya rage wa Leverkusen dama a kokarinta na zama ta hudu a teburin gasar.

—Ruwan kwallaye a Frankfurt

A wasan da aka buga tsakanin kungiyoyin Eintracht Frankfurt da Freiburg a filin wasa na CommerzBank Arena kuma an tashi da ci 3-3. Freiburg ce dai ta fara cin kwallo kafin Frankfurt ta farke a minti na 35.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne Freiburg ta yi azama ta jefa kwallaye biyu a jere. Ana minti 79 ita ma Frankfurt din da ba ta bari an bar ta a baya ba ta farke kwallayen inda aka tashi canjaras.

—Leipzig ta gaza kaiwa ta biyu a teburi

Kunnen dokin da kungiyar RB Leipzig ta buga 2-2 da kungiyar Hertha Berlin ya hana ta zama ta biyu a teburin gasar ta Bundesliga.

Hakan ya sa za ta ci gaba da kasancewa ta uku a bayan Dortmund da maki 55.

Jan katin da dan wasanta Halstenberg ya samu ya rage mata kaimi inda kuma burin nata na kaiwa matsayi na biyu a teburin ya ci tura.

Kwallon da dan wasan Hertha din, Piatek ya farke a minti 82 a bugun fenariti ne ya dakushe burin na Leipzig.

—Sauran wasanni

Werder Bremen 0-0 Burossia Monchengladbach
Augsburg 0-0 SC Paderborn
Fortuna Dusseldorf 2-1 Shalke 04
Hoffenheim 3-1 FC Koln
Union Berlin 1-1 Mainz 05

A yau za’a kara tsakanin Stuttgart da Hamburger SV.