A karshen makon da ya gabata ne dai aka fafata wasannin mako na 10 na gasar Firimiyar Ingila da ake yi wa lakabi da English Premier League (EPL).
Aminiya ta zakulo muku wasu wasannin da suka fi daukar hankali wadanda aka fafata a ranar Asabar da Lahadi.
Chelsea da Wolves
Chelsea ta doke Wolverhampton 3-0 a wasan da suka fafata ranar Asabar a Stamford Bridge.
Wadanda suka ci wa Chelsea kwallayen sun hada da Kai Havertz da Christian Pulisic da kuma Armando Broja.
Kenan Havertz ya ci kwallo na 50 a tarihin sana’arsa ta murza leda, mai 36 a Bundesliga da 14 a Firimiyar Ingila
Wannan shi ne wasan farko da Graham Potter ya ja ragamar Chelsea a Stamford Bridge a Firimiyar Ingila.
Tsohon kociyan Brighton ya maye gurbin Thmosa Thucel, wanda Chelsea ta kora a bana, bayan da ya kasa taka rawar gani.
Kawo yanzu Potter ya ja ragamar wasa hudu da cin uku da canjaras daya, har da cin Milan 3-0 a Gasar Zakarun Turai.
Wolves ta buga wasan a karon farko, bayan da ta sallami kociyanta Bruno Lage.
Haka kuma Diego Costa ya buga wa Wolves wasan, inda ya fuskanci tsohuwar kungiyarsa.
Costa ya ci kwallo 52 a wasa 89 da ya yi wa kungiyar Stamford Bridge daga 2014 zuwa 2019.
Manchester City da Southampton
Manchester City ta dare mataki na daya a kan teburin Premier League, bayan da ta doke Southampton 4-0 ranar Asabar a Eihad.
City ta ci kwallo a minti na 20 da fara wasa ta hannun Joao Cancelo, minti 12 tsakani Phil Foden ya ci na biyu na biyar da ya zura a raga a kakar nan.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne City ta ci gaba da cin kwallo ta hannun Riyad Mahrez, sannan Erling Haaland ya kara na hudu na 15 da ya ci a bana.
Da wannan sakamakon City ta koma ta daya a kan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 23, bayan buga wasa tara.
Sai dai Arsenal ta karbe gurbinta, bayan ta karbi bakuncin Liverpool a Emirates a karawar mako na tara mai maki 21.
Liverpool wadda ta yi wasa bakwai tana ta 10 da maki 10, kafin tashi wasan Brighton da Tottenham da ake yi ranar Lahadi da Yammaci.
Arsenal ta koma matakinta, ta lallasa Liverpool a Emirates
Arsenal ta ci Liverpool 3-2 a wasan mako na 10 a Firimiyar Ingila ranar Lahadi a Emirates ta koma ta daya a teburin gasar.
Arsenal ce ta fara cin kwallo a kasa da dakika daya da fara wasa ta hannun Gabriel Martinelli.
Karon farko da Arsenal ta ci kwallo a karamin lokaci da take leda a Firimiyar Ingila a gida tun bayan Oktoban 2011 lokacin da Robin van Persie ya ci Sunderland a dakika 29 da fara wasa.
Haka kuma wannan ne karon farko da Arsenal ta ci Liverpool a kankanin lokaci da fara wasa a Firimiyar a tarihi.
Liverpool ta farke ta hannun sabon dan wasan da ta dauka a bana, Darwin Nunez a minti na 34.
Daf da za suje hutu ne, bayan karin lokaci Gunners ta kara na biyu ta hannun Bukayo Saka, hakan suka yi hutu Arsenal da ci 2-1.
Suna komawa zagaye na biyu ne Liverpool ta farke ta hannun Roberto Firmino, kuma na shida da ya zura a raga a bana a Firimiyar.
Daga baya Arsenal ta ci kwallo na uku ta hannun Saka a bugun fenariti, bayan da aka yi wa Gabriel Jesus keta.
Kwallo na 20 kenan da Saka ya zura a raga tun fara buga wasannin Premier, ya kuma zama matashi na biyu da ya ci 20 a Arsenal, bayan Nicolas Anelka wanda yake da shekara 20 da kwana 41, Saka yana da shekara 21 da kwana 34..
Gabriel Martinelli ya zama matashi na farko da ya ci kwallo ya kuma bayar aka ci Liverpool a Firimiyar mai shekara 21 da kwana 113,
Dan kasar Brazil yana da hannu a cin kwallo 10 a wasa 14 da ya buga a babbar gasar tamaula ta Ingila, wanda ya ci biyar ya kuma bayar da biyar aka zura a raga.
Arsenal ta koma matakinta na daya da maki 24 da tazarar maki daya tsakaninta da Manchester City ta biyu.
Ita kuwa Liverpool ta hada maki 10 tana tana kuma ta 10 a teburin Firimiyar Ingila na kakar nan.
Manchester United da Everton
Manchester United ta yi nasara a kan Everton da ci 2-1 a babbar gasar tamaula ta Ingila a Goodison Park.
Cristiano Ronaldo ne ya ci na biyun, kuma kwallo na 700 a tarihin kungiyoyin da ya buga wa tamaula.
Ronaldo ya fara daga zaman benci a karawa da Everton ranar Lahadi daga baya ya canji Anthony Martial, wanda ya ji rauni a minti na 29.
Everton ce ta fara cin kwallo a minti na biyar da take leda ta hannun Alex Iwobi, minti 10 tsakani United ta farke ta hannun Antony.
Kwallon farko da dan wasan tawagar Portugal mai shekara 37 ya ci a gidan Everton tun bayan 2005.
Yadda Ronaldo ke ci gaba da jan zarensa
Kwallo da ya jefa a wasan shi ne biyu da Ronaldo ya ci a bana, inda ya zura na farko a raga a Europa League da Sheriff FC, kuma na 699 da ya ci a lokacin cikin watan Satumba.
Kyaftin din Portugal ya ci wa Manchester United kwallo 144 a karo biyu da yake buga mata wasanni.
Ya ci wa Real Madrid 450 da 101 da ya zura a raga a fafatawar da ya yi wa Juventus da kuma biyar da ya ci a lokacin da ya taka leda a Sporting Lisborn.
A bara Ronaldo ya kafa tarihin zama na daya a yawan ci wa tawaga kwallaye a duniya.
Kwallo biyun da ya ci Jamhuriyar Ireland ya sa ya hada 111 jumulla, hakan ya haura tarihin da Ali Daei ya kafa mai 109 a raga a tawagar Iran tsakanin 1993 zuwa 2006.
Haka kuma shi ne na gaba a cin kwallaye a Champions League mai 140 – ya bai wa Lionel Messi abokin hamayyarsa tazarar 13.
Haka kuma Ronaldo yana gaban Messi a yawan cin kwallaye a kungiyoyin da yake buga wa wasanni, bayan da kyaftin din Argentina keda 691 a fafatawar da ya yi Barcelona da Paris St Germain.