✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda sojojin Najeriya suka hallaka ’yan Boko Haram a Gwoza

Sojoji sun dakile harin mayakan tare da aika su lahira a garin na Gwoza

Mayakan kungiyar Boko Haram da suka kai hari a Garin Gwoza na Jihar Borno sun kwashi kashinsu a hannun sojojin Najeriya.

Wata majiya mai tushe da Aminiya ta tatattauna da ita a garin ta ce mayakan na Boko Haram sun shigo garin ne ta bangaren Gabas, a lokacin ana shirin yin Sallar La’asar.

“Zaratan sojojin Najeriya sun dakile harin nasu, tare da hallaka biyar daga cikinsu.

“Maharan yara ne kanana masu matsakaicin shekaru, wanda ke nuni da cewa ’yan Boko Haram na ci gaba da amfani da yara kanana wajen aiwatar da ayyukan ta’addancinsu.” inji majiyar da ke da zama a garin na Gwoza.

Wani bidiyo da yake yawo a kafafen sada zumutan ya nuna yadda kananan yara da mutanen gari ke murna da kuma jinjina wa sojojin tara da yin Allah wadai da mayakan da suka kai harin na ranar Talata.