✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda Sojoji Suka Ragargaza ’Yan Boko Haram Da Dama A Borno

Dakarun Operation Hadin Kai (OPHK) sun hallaka ’yan ta’addan Boko Haram da daman gaske  a wata arangama da suka yi a Ngowom da ke Karamar…

Dakarun Operation Hadin Kai (OPHK) sun hallaka ’yan ta’addan Boko Haram da daman gaske  a wata arangama da suka yi a yankin Ngowom da ke Karamar Hukumar Mafa ta Jihar Borno.

Majiyarmu ta tsaro ta ce an kashe ’yan ta’addan ne a yayin da suke tafiya da ayarin motocinsu wasu kuma a kan babura kimanin  20 daga yankin Arewacin jihar zuwa yankin Mafa, za su je Dajin Sambisa.

Wata majiyar leken asiri ta ce sojojin sun ragargaje su ne bayan samun sahihan bayanan sirri na cewa ’yan ta’addan na tafiya a mashigin Mafa.

Dakarun tare da hadin gwiwar mayakan sa kai na Civilian Joint Task Force sun yi wa ’yan ta’adda kwanton bauna, suka kashe da yawa daga cikinsu.

Wani kwararre a fannin yaki da tada kayar baya a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya ce sojojin sun kama wani dan ta’adda da ransa, yayin da wasu suka gudu da harbin bindiga a jikinsu.

Ya ce wasu jami’an CJTF guda biyu sun samu raunuka yayin wata musayar wuta da aka yi da su, inda da aka kwato makamai da babura daga hannun ’yan ta’addan.