✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda Sojoji Suka Ragargaza ‘Yan Bindga A Zamfara

Sojiji sun kashe ’yan bindiga da yawa, sun kuma yi asarar jami’ansu uku a wani kwanton bauna da ’yan ta'ada suka yi musu a Karamar…

Sojiji sun kashe ’yan bindiga da yawa, sun kuma yi asarar jami’ansu uku a wani kwanton bauna da ’yan ta’ada suka yi musu a Karamar Hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara ranar Laraba.

Mazauna yankin sun ce ’yan bindgar sun yi kwanton bauna ne a yayin da sojojin ke kan hanyarsu ta kai dauki ga kauyukan Fanda-Haki da ‘Yar Katsina da kuma Kararakai da ’yan bindigar ke shirin kai hari.

A cewar Hussaini Ali, wani mazunin yankin, sojojin na tsaka da tafiya ne sai kawai suka ji an bude musu wuta, suka mayar da martani, inda suka hallaka ’yan bindiga da yawa, wanda haka ta sa dole bata-garin bindigan suka tsere.

Ya ce a sakamakon haka mutanen yanki na zaman dar-dar, ganin irin barnar da sojoji suka yi wa ’yan ta’addar, mutane na tsoron za su iya hucewa a kansu.

“Alhamis ranar kasuwa ce a Bingi amma ’yan kasuwa suna fargabar zuwa cin kasuwar saboda komai  na iya faruwa,” a cewar Ali.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar Sojin da ke jihar, Kyaftin Ibrahim Yahaya, amma haka ba ta samu ba, saboda kiran ba ya shiga.