✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda sojoji suka hallaka ’yan ta’adda 8 a Kaduna

Sojoji sun hallaka ’yan ta'adda takwas a wata arangama a Karamar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.

Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda takwas a wata arangama a Karamar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.

Sojojin sun aika su lahira ne a yankin Kampanin Doka, lokacin da dakarun suke gudanar da sintiri, inda suka iske bata-garin sun kai hari.

Ma’aikatar tsaron jihar Kaduna ta ce, nan take sojoji suka kashe bakwai daga cikin maharan, suka kwato makamai a hannunsu.

Kwamishinan ma’aikatar, Samuel Aruwan, ya ranar Alhamis cewa sojojin sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda uku da harsasai sama da 120 da na’urorin sadarwa da wasu makamai da ababen hawa daga hannun ’yan bindigar.

Aruwan a ce sojoji sun kuma hallaka wani dan bindiga a yayin wani sintirin da suka gudanar a yankin Gayam, sauran ’yan ta’addan kuma suka tsere da raunukan harbi.

Gwamnan jihar, Uba Sani ya ya jinjina wa sojojin bisa wannan kokari da nasara da suka samu.