Wasu hare-hare da jiragen Rundunar Sojin Sama ta Najeriya samfurin Super Tukano suka kai, sun kashe nayakan Boko Haram da dama a Shehutari da Mantari a karamar hukumar Bama ta jihar Borno.
Mayakan sun sha luguden ne a ranar Talata bayan sun taru domin gudanar da addu’o’i na musamman ga kwamandojinsu da mayaka 103 da jiragen yaki suka kashe mako guda kafin nan.
- Jiragen yaki sun kashe ’yan ta’adda 100 a rana guda a Borno
- Sojoji sun kashe ’yan ta’addan ISWAP 140 a watan Disamba
Wata majiyar tsaro ta ce Rundunar Operation Hadin Kai ta kama ’yan ta’adda da dama a Shehutari, bayan wadanda ta aika lahira.
Majiyar ta ce ’yan ta’addan da dama sun samu raunuka inda aka kan su suna ta gudu ta bangarori daban-daban a dokar daji a don tsira da rayukansu.
Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Tafkin Chadi, ya ce ana jinyar ’yan kungiyar da dama da suka jikkata a wani wuri a Yammacin Mantari.
Hare-haren jiragen soji sun karya lagon kungiyar Boko Haram sosai a Dajin Sambisa.
A ranar Kirsimeti, kwamandan Boko Haram, Ali Ngulde ya tura mayaka karkashin jagorancin Amir Muke daga Tsaunin Mandara da Abu Hassana, domin ta’aziyyra mayakan da sojoji suka hallaka.
A hanya ne su sojojin suka ritsa su, suka aika su lahira, kamar wadancan din, wasu kuma suka sha da kyar.
Daga baya mutun takwas daga cikin mayakan da suka samu raunuka sun mutu.