✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda siyasa da rashin aikin yi ke ta’azzara shaye-shaye a Kano

Kano kamar cibiya ce ta neman lafiya, amma likitocin ƙwaƙwalwan da ke Kano ba su wuce 10 ba.

Daddy da wasu matasa sun yi fice a wani yanki a cikin birnin Kano, inda suke haɗuwa domin shaye- shayen kayan maye.

Wannan yanki yana cikin unguwar Yakasai ne, wata unguwa da ke tsakanin Ƙofar Nasarawa da Ƙofar Mata a tsakiyar birnin Kano.

Daga isa wajen da suke haɗuwa, ƙaurin hayaƙin tabar wiwi da sigari ne zai tarbi mutum, wanda wata alama ce da ke nuna cewa an zo yankin nasu.

Bayan wannan alamar marabar ta hayaƙin tabar wiwi da na sigari, wajen na cike da ƙazanta da yanayi mara kyau.

A wajen ne wakilinmu yi ci karo da Daddy, matashi mai shekara 23, a yayin da yake ta’ammali da kayan maye da suka kama da tabar wiwi da ƙwayoyi da kuma kodin.

Ya bayyana cewa, ya samu gata daidai gwargwado, amma yanayin unguwar da ya taso ne ya kwaɗaita masa shiga rayuwar mu’amala da kayan maye tun yana da shekara tara.

A cewarsa, “mun taso cikin unguwa da tun muna yara muke ganin ana daba da sare-sare ne.”

Ko a lokacin da yake yi wa wakilinmu jawabi, yana riƙe da tabar wiwi a hannun dama da kwalbar kodin a ɗayan hanun.

Ya ƙara da cewa, tun yana makaratar firamari ya fara jarrabawa da allin rubutu daga bisani ya fara ziyartar wuraren da ake shaye-shayen.

Zunzurutun matasan ne a cike a wanan dandalin yayin da suke sharholiyarsu da miyagun ƙwayoyi nau’uka daban-daban.

Harkar shaye-shaye ba maza ne kawai ke yi ba

Jaridar Aminiya ta zanta da Zara’u, wata matashiya mai shekara 32 a titin Niger da ke Sabon Gari a Jihar Kano.

Ta bayyana wa jaridar yadda ta fara mu’amala ka kayan maye bayan mutuwan aurenta.

Tana zaune ne a wannan yankin da ɗanta cikin wasu mata masu zaman kansu.

Cikin ɗakinta, wanda ke cike da ƙawayenta mata, wakilinmu ya iske su ne a lokacin da suke haɗa kodin da lemon kwalba suna afawa bi da bi kuma ko gezau.

“Ina shan kodin da wiwi da sigari da roce domin in samu kwanciyar hankali ne.

“Ƙaddara ce da mutuwar aure ta kawo ni nan inda nake zaune da sauran mata,” a cewar Zara’u.

Masana sun bayyana damuwa a kan yadda ƙiddidigar shaye-shaye ke nuna yadda matasan Jihar Kano, garin da ke da ɗimbin tarihi da kuma alfahari da yawan matasa ke ƙara hauhawa.

Amma matsalar shaye-shaye ba ta Kano ce kawai ba.

Rahoton shekarar 2018 na ofishin kula da miyagun ƙwayoyi da laifuffuka na Majalisar Ɗinkin Duniya ya nuna cewa, yawan mu’amala da kayan maye ya kai kashi 14.4 a Nijeriya.

Wannan yana nufin cewa, aƙalla mutum miliyan 14.3 da ke tsakanin shekara 15 zuwa 64 a Nijeriya na yin mu’amala da miyagun ƙwayoyi.

Haka kuma ƙididdigar ta nuna cewa, maza sun fi yin mu’amala da ƙwayoyi, amma a duk cikin mata huɗu, ɗaya na mu’amala da kayan maye.

Rahoton ya ƙara da cewa, ƙididdigar Nijeriya kaɗai ta fi ƙididdigar da rahotun ofishin ta yi a 2016 na duniya baki ɗaya.

A cewar rahoton 2018, Jihar Kano ce ke kan gaba a yankin Arewa maso Yamma, yayin da take ɗauke da kaso 12 wanda ke nuna cewa aƙalla mutum miliyan uku ne a yankin Arewa maso Yamma, a shekarar da ta gabata suka yi mu’amala da kayan maye.

Cikin wannan ƙididdiga, mutum miliyan ɗaya suka yi mu’amala da kayan maye a lokacin.

A yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Gabas, Jihar Kwara da Gombe ne ke kan gaba da kaso 13 da 21.

A yankunan Kudu maso Kudu, Kudu maso Gabas da kuma Kudu maso Yamma, Jihar Delta na da kaso 18, Imo na da 18.1, yayin da Legas da Oyo na da kaso 20 da 15.3 a bara.

Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA), Buba Marwa, a 2021 ya bayyana cewa, Kano na da mutum miliyan biyu da ke ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.

Ya ƙara da cewa, ƙididdigar ta nuna cewa, cikin kowane mutane shida a jihar, ɗaya na shaye­shaye.

A cewar Farfesa Maikano Madaki, wani masanin ilimin zamantakewa a Jami’ar Bayero da ke Kano, ya bayyana cewa, matsaloli kamar rashin aikin yi da gurɓacewar tarbiya da bangar siyasa na daga cikin abubuwan da ke ƙara ingiza matsalar shaye-shaye a Jihar Kano.

“Idan ka kalli matsalar daga yanayin zamantakewa a cikin gida, za ka ga cewa gurɓacewar tarbiya da rashin wadatacciyar kulawar iyaye ko kwaɓa da kuma yawan mutuwar aure, ke ƙara haɓaka matsalar shaye-shaye a Jihar kano,” a cewarsa.

Ya ƙara da cewa, “wasu gurɓatattun ’yan siyasa na ba da gudummawa wajen ƙarfafa harkar shaye-shaye a Kano domin suna amfani da matasa a matsayin ’yan bangar siyasa.

“Haka kuma bangar siyasa ba ta yuwa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, dole sai da miyagun ƙwayoyi. Su ’yan siyasar ke sama masu suna ba su,”

Neman mafita ta hanyar zamani da na gargajiya

Fatima Idris (an canja suna) ta fara shaye-shaye ne lokacin da ta gwada shan crack, wani nau’in sinadarin hodar ibilis da ke da wahalar sakin mutum idan ya bi jikinsa.

“Da farko, ban san ko mene ne ba. Kawai gani na yi ƙawayena suna sha, shi ne na jaraba.

“Ana kiran ta da crack kuma ana zuƙar hayaƙinta ce,” a cewarta lokacin da jaridar Aminiya ta ziyarce ta a gidan gyaran hali na Hukumar Hana Sha da Fataucin

Ƙwararriyar likitar ƙwakwalwa a Asibitin Aminu Kano, Dokta Asma’u Garko ta ce, a Kano mata ba su cika neman taimako wajen magance matsalar shaye­shaye ba saboda gudun kar a ƙyamace su.

A cikin gidan gyaran halin, Aminiya ta zanta da Dauda Auwal, wani matshi da ke da burin zama babban ɗan kasuwa tun yana yaro, amma shaye-shaye ya hana shi cika burinsa, ya bayyan cewa, mu’amala da hodar ibilis ce ta sa ya zo neman mafita a gidan gyaran halin.

Auwal ya kwashe tsawon shekara 18 yana ta’ammali da hodar iblis.

“Abokan banza ne da zuwa gidan rawa. Muna zuwa gidajen rawa sai mu ɗan sha.

“A tunaninmu, abun burgewa muke yi, ashe shi ne zai janyo muna wannan matsalar da na faɗa.”

A lokacin da Auwal da Fatima suke neman mafita ta hanyoyin zamani, wasu na neman mafita ta hanyoyin gargajiya da na addini.

A garin Kano da ke bin dokar shari’ar Musulunci, ana ba da taimakon shaye-shaye na addini.

Cibiyar ba da magani ta fuskar addini wato Kachako Islamic Medicine Centre, da ke da ragista da Hukumar NDLEA na ɗaya daga cikin cibiyoyin da ke nema wa masu fama da matsalar ta shaye-shaye lafiya a Jihar Kano.

A cewar shugaban cibiyar, Malam Yakubu Kachako, tun da aka kafa cibiyar a 2018, ba a taɓa amfani da mari ba.

Kuma duk bayan wata uku, cibiyar na yaye mutum 20 tare da koya masu karatun Al’ƙurani.

“Tun kafa wannan cibiya, mun yaye sama da mutum 300. Tsarinmu ya bambanta da na asibiti domin su suna duba matsalar ce ta fuskar lafiyar ƙwaƙwalwa.

“Mu kuma bayan mun duba abun ta matsalar ƙwaƙwalwa, muna duba abun ta fuskar mutanen ɓoye,” a cewar Dokta Kachako.

Ya ƙara da cewa, bayan sun kai masu matsalar ta shaye-shaye asibiti domin yin gwaje-gwaje, sai su dawo su bibiyi abun ta hanyar gargajiya da addu’o’i.

Darakta Janar na Hukumar Hisba ta Jihar Kano, Abba Sufi ya bayyana wa jaridar Aminiya cewa, hukumar na iya ƙoƙarinta wajen magance matsalar shaye­shaye a Jihar Kano domin yana daga cikin ayyukan hukumar na hani da munanan ayyuka tare da kwadaita kyakkyawa.

Yadda dillalai ke kasuwanci kayan maye a filin wasan Sani Abacha

Ƙananan diloli su ne mafi kusa da masu mu’amala da kayan maye.

A cewar Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Nijeriya, su ne ake gani a wasu wurare da ke cikin al’umma, suna siyar da abubuwan da ka iya cutar da masu amfani da su.

Domin gane yadda masu sayarwa ke hada-hadar kayan maye a Kano, wakilinmu ya ziyarci filin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata, ta hanyar ɓatar da kama a matsayin wanda ke son sayan kayan mayen.

Misalin ƙarfe 5 na yamma a watan Afirilu ne wakilnmu ya ziyarci fillin wasan.

Yayin da yake kutsawa ta ƙarƙashin inda masu kallon wasa suke zama, kwalaben kodin da fankon ƙwayoyi ne ke ko’ina a ƙasa.

Daf da inda matasan suke kasuwancinsu, ko’ina ya turnuƙe da warin hayaƙin tabar wiwi da na sigari.

Matasa sun kafa da’irori daban-daban yayin da wasu ke cinikayyarsu, wasu na ci gaba da afa kayan maye daban-daban a baki.

Masu sayarwa, wasu a tsaye, wasu kuma na zaune a gaban kayayyakin mayen da suka baje a ƙasa.

Ababen sa maye kamar kodin da tabar wiwi da ƙwayoyi kamar eɗol da roche da dai sauransu ke shimfide a ƙasa.

Binciken jaridar Aminya ta nuna cewa, kayayyakin mayen da ake sayarwa a filin wasu sun kama daga kodin na kamfanin MaxCoff da Bronclear, tabar wiwi, tabar Kush da kwayoyi kala-kala kamar exol, roche, diazapam da tramol.

Bincike ya ƙara nuna cewa, ana sayar da kodin din Maɗcoff da Bronclear a Naira 6000 zuwa Naira 7000 yayin da ƙwayoyi kamar roche duk kati a kan Naira 1,200, exol Naira 50 duk guda ɗaya Diazepam kuma Naira 200 duk guda ɗaya.

Masani kan harka ƙwayoyi, Kim Bot ya ce, duk ƙwayoyin nan da ake sayarwa a wajen, sai da takardun asibiti ake sayar da su.

Kim ya ƙara da cewa, ana amfani da Diazepam ne wajen magamce matsalar shan giya da tsananin damuwa.

Ya ƙara da cewa, ana amfani da eɗol ne wajen magance matsalar jijiyoyin jiki. “Shi Roche ba haramtaccen magani ba ne domin sai da nazari sosai ake ba wa mara lafiya shi domin zai iya yin ajalin mutum ko ya sa dogon suma,” inji shi.

Duk da illolin wadannan ƙwayoyi, matasa na ci gaba da sha da sayarwa a filin wasan ba tare da damuwa ba.

‘Wani sabon kayan maye mai hatsari’

Mu’amala da kayan maye babbar matsala ce a Jihar Kano a cewar Dokta Asma’u Garko, likatar ƙwaƙwalwa a Asibitin Aminu Kano kuma ƙwararriyar mai ba da shawara a kan ta’amali da miyagun ƙwayoyi.

Dokta Garko ta bayyana wa Aminiya cewa, wani nau’in kayan maye da ake kira ‘Ice’ ya shigo garin Kano kuma matasa na saya suna amfani da shi kuma hakan na iya ingiza matsalar ta shaye-shaye a jihar.

“Baban abun damuwa shi ne wannan nau’in kayan maye na da hatsari fiye da hodar ibilis.

“Mun san cewa hodar ibilis na da illa sosai amma wannan ya fi ta illa da kusan kaso huɗu.

Tunda na fara aiki a matsayin likitar ƙwaƙwalwa a wannan asibitin, ba mu taɓa samu irin wannan nau’in abun mayen ba.

“Amma abin da ya firgita ni, cikin mutum bakwai da muka gwada don sanin irin abubuwan da suke sha, guda hudu na amfanin da wannan ƙwayar ta ‘Ice’ din.”

Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Jihar Kano, Abubakar Ahmad ya bayyan wa Aminiya cewa, suna ta yin nasarar cafke miyagun ƙwayoyi.

Ya ƙara da cewa, hukumar a cikin wata uku a shekarar nan, ta kama ƙwayoyin tramol miliyan biyar.

Ya kuma bayyan wa Aminiya cewa, sun yi nasarar cafke manyan dillalai guda 319, wadanda cikinsu akwai mata 19 masu siyar da kayan maye.

“Cikin abubuwan da muka kama, mun ƙwace tabar wiwi mai nauyin kilo 2,321,000 da wasu kayayyakin da suka hada da kodin da ƙwayoyi da sauransu masu nauyin kilo 2,446,000.

“Wannan yana nuna irin nasarar da muka yi don fitar da kayan maye mai wannan yawa. Idan ba mu yi nasarar ƙwace wannan ƙwayoyin ba, ba ƙaramar illa za su haifar a ciki al’umma ba,” inji kwamandan.

Hukumar ta ce, za ta ci gaba da ƙwace kayan maye tare da kama masu sayarwa da ruwa da tsaki a harkar domin rage matsalar a jihar.

Abin da gwamnati za ta yi — Masana

Shugaban Asibitin Lafiyar Ƙwaƙwalwa na Dawanau a Jihar Kano, Farfesa Auwal Salihu ya ce, duk da cewa ba a dade da bude asibitin ba, jami’an da kayan aikin da ke ƙasa ba za su iya kula da mafi ƙanƙanta mutane masu fama da matsalar shaye­shaye a Jihar Kano ba.

“Gadajen da muke da su ba za su isa mu  kwantar da masu irin wannan mastalar ba, idan sun zo asibiti neman magani.

“Akwai buƙatar gadaje da ma’aikata da za mu yi amfani da su wajen kula da masu shaye­shaye.

“Domin asibitin cibiya ce ta horar da likitoci da kuma daliban lafiya don haka muna sa ran gwamnati za ta duba lamarin nan ba da jima wa ba,” inji farfesa Auwal.

Shugaban asibitin ya ƙara da cewa, ya kamata a riƙa koyar da yara illolin shaye­shaye tun daga makaratun firamare domin daga irin shekarun suke fara koyon mu’amala da kayan maye.

Dokta Asma’u ta ƙara da cewa, Kano na fama da ƙarancin ƙwararrun likitocin ƙwaƙwalwa masu duba wadanda suke mu’amala da kayan maye.

“Kano kamar cibiya ce ta neman lafiya, amma likitocin ƙwaƙwalwan da ke Kano ba su wuce 10 ba,” inji ta.

Ta ƙara da cewa, a Kano masu ƙaramin ƙarfi da kuma matan da ke fama da wannan matsala ta shaye-shaye ba sa iya neman maganin dalilin tsadar da kulawar ke da shi.

“A Kano dai, ba mu da inda aka ware na kula da mata masu fama da matsalar shaye­shaye, amma akwai na maza.

“Muna hada matan ne da sauran mata masu matsalar ƙwaƙwalwa duk da cewa matsalolinsu sun bambanta.”

Dokta Yakubu Kachako, mai cibiyar Kachako Islamic Medicine ya ce, sai an cire gidan gyaran hali na Kiru daga Ma’aikatar Mata da ci gaba na jihar Kano.

Ya yin da yake ba da shawara ya ce, za a iya yi wa Kiru hukumar da za ta riƙa kula da ita domin ta ci gashin kanta.

Akwai alamun nasara

Masu fama da matsalar shaye-shaye na iya warkewa kuma su daina kamar yadda Sani Sani, mamba daga cikin wata ƙungiyar matasa masu wayar da kan al’umma kan illolin shaye-shaye mai suna YAFODA ya bayyana.

Sani ya yi fama da matsalar crack, wani nau’i na hodar ibilis.

“Na sha wuya kafin na daina shaye-­shaye. Ina ta ragewa ne a hankali yayin da nake ta zuwa nema magani”.

Yanzu Sani ya zama ɗan kasuwa, inda yake sayar da waya a kasuwar Farm Centre da ke cikin Kano.

“Da ina sha kamar sau goma a rana sai na dawo sha sau biyar. Daga nan na rage zuwa sau dayya har Allah Ya taimake ni, na daina. Amma kafin na daina gaskiya na sha wahala sosai,” inji Sani.

Daraktar Jin Daɗin Al’umma na Ma’aikatar Mata a Jihar Kano, Hajiya Binta Yakasai ta ce, Gwamnatin Kano na iya ƙoƙarinta domin magance matsalolin shaye-shaye a jihar.

Ta ce gwamnatin na ƙara fadada gidan gyaran hali na Kiru domin magance matsalar.

Da jaridar Aminiya ta ziyarci gidan gyaran hali na Kiru, babu majinyanta, sai dai jami’an da ke wajen sun ce an sallame su ne domin gudanar da aikin gyare-gyaren da ake yi.

Amma bincike ya nuna cewa, a 2019, Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta ce ta kashe wa Kiru Naira miliyan 128 domin bunƙasa wajen da fadada shi.

Yanzu kuma, Gwamnatin Abba Kabir ta ware Naira miliyan 107.6 domin sake gyara makarantar.

Amma Yakasai ta ce, wannan gwamnatin da gaske take domin ganin cewa an magance matsalar ta shaye-shaye a Kano.

“Idan aka kammala gyaran, za a riƙa koya wa matasa aikin kafinta, tela, walda, kiwon kaji da wasu ƙananun sana’oi domin ci gaban rayuwarsu bayan sun fito daga Kiru,” inji ta.

Ta yi gargadin cewa, Gwamnatin Kano ba za ta laminci harkar shaye-shaye ba domin za ta dauki tsatsaurar mataki a kan duk wanda aka kama yana ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ko sayarwa.

Wannan binciken Gidauniyar Daily Trust ce ta ɗauki nauyin tare da gudunmawar Gidauniyar MacArthur