✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda shugaban masu fasa bututun mai ya tsere daga kurkuku a Meziko

Maharan sun fasa gidan yarin da motarsu kafin su tsere da fursunoni

’Yan bindiga sun kai hari a wani gidan yarin da ke birnin Tula na kasar Meziko inda suka kubutar da shugaban masu fasa bututun mai suna satar man fetur da wasu fursinoni takwas.

Ministan Harkokin Cikin Gidan Kasar Meziko, Simon Vargas, ya ce maharan sun fasa gidan yarin ne sannan suka kubutar da mutanen.

Ana zargin yaran gawurtaccen mai fasa bututun man ne suka kai harin domin su kubutar da shi daga gidan yarin na birnin Tula, mai babbar matatar mai.

Hukumomin ’yan sanda a birnin Tula sun tabbatar cewa jami’an tsaron kurkukun biyu sun sun samu rauni a harin.

Wasu majiyoyi a kasar sun tabbatar cewa maharan sun tayar da bom a wata mota a lokacin, amma dai babu tabbacin hakan a hukumance.

Ministan ya ce da farko maharan sun ajiye motocinsu biyu a kusa da babbar kofar shiga kurkukun domin su dauke hankalin jami’an da ke tsaron kofar.

A yayin da hankalin jami’an tsaron ya koma kan motocin da maharan suka cinna wa wuta, sai bata-garin suka zagaya zuwa wani bangaren gidan yarin, inda suka yi amfani da motarsu suka fasa ginin.

Hukumomin ’yan sanda sun ce bayan fasa gidan yarin, motoci da dama ne suka shiga domin tserewa da shugaban masu fasa bututun man da wasu fursunoni takwas da ke tsare a gidan gyaran halin.

Kafofin yada labaran kasar sun ce a kwanakin baya ne jami’an tsaro suka yi nasarar cafke shugaban gungun barayin man fetur din kafin a tsare shi a gidan yarin.

Ana yawan samun gobarar bututun mai a kasar Mezico a sakamakon ayyukan barayin da ke fasa bututan domin su saci man fetur.