✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Sarki Sanusi II ya sauka jihar Legas

A cikin daren ranar Juma’a tsohon sarkin Kano ya isa birnin Legas, inda ya sauka a tashar jiragen saman Murtala Muhammed International Airport (MMIA) bayan…

A cikin daren ranar Juma’a tsohon sarkin Kano ya isa birnin Legas, inda ya sauka a tashar jiragen saman Murtala Muhammed International Airport (MMIA) bayan ya tashi daga filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe a Abuja da misalin karfe 10:30 na dare a jirgin da ya yi shata na kamfanin Quits Aviation mai lamba N5500JF.

Tsohon sarkin Kano ya samu tarba daga matansa da ‘ya’yansa da wasu daga cikin ‘yan uwa da abokan arziki, ya bar tashar jirgin saman da misalin karfe 12:17 na dare.

Malam Muhammadu Sanusi, ya yi murmushi a lokacin da ‘yan jaridu suka so ya yi tsokaci akan dawowarsa Legas biyo bayan al’amuran da suka wakana sai dai bai ce uffan ba, ya yi murmushi kawai ya shiga mota mai lambar Legas, APP 674 FU wacce ta fice da shi daga filin jirgin saman zuwa gidansa da ke cikin birnin Legas.

Sanusi II bayan sauka filin jirgin saman Legas