Kididdiga ta nuna cewa a cikin shekaru biyar sojin Najeria sun aiwatar da yake-yake 40 masu sunaye daban-daban domin magance matsalolin tsaro, amma har yanzu ba a kawo karshen abun ba. Hakan na dauke ne a alkalumman da Aminiya ta tattaro.
Wasu masana sun ce sa wa salon yakin suna ba wani abu ba ne, wasu kuma na ganin hakan shirme ne domin babu wani sauyi da abun ya kawo sai kara durmiya da sassan kasar ke yi cikin matsaloli iri-iri na tsaro.
- Matsalar tsaro: Obasanjo ya bukaci a sauya tsarin Najeriya
- ‘Yakin Najeriya a Laberiya ne silar rashin tsaro a teku’
- Lawan ya gaya wa Buhari yadda zai kori hafsoshin tsaro
A tsawon shekaru biyar da suka gabata, Sojin Kasa da na Sama da kuma na Ruwa na da dalilan da za su bayar na yi wa yake-yaken da suka yi da suka hada da na magance ta’addanci da garkuwa da mutane da tsagerun Neja Delta; rikincin manoma da makiyaya; da kashe-kashen babu gaira babu dalili da dai sauransu.
Aminiya ta gano yadda jami’an tsaro suka aiwatar da salon yaki iri-iri cikin shekaru biyar a rukunin farko da na biyu da kuma na ukku.
Sai dai duk da salon yakin da sojin suka aiwatar domin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa, masu kai hare-haren ba su daina ba kuma a kullum sabon salo matsalar ta rashi tsaro ke dauka a kasar.
Bahari ya nuna bacin ransa
A kwanakin baya ne Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna bacin ransa tare da zare wa Hafsoshin tsaron kasa ido cewa ba su yin abin da ya dace a kan harkar tsaron.
Babban Mai ba Shugaban Kasa Shawara a kan Harkokin Tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno, a tattaunawar bayan taro da suka yi da Buhari ya bayyana wa ‘yan jarida cewa “Shugaban Kasa ya nuna tsananin damuwa kan tabarbarewar yanayin tsaro a kasar nan”.
Ya kuma kara da cewa, Buhari ya ba da umarnin su gaggauta sauya salon magance matsalolin tsaron domin dakile yaduwar ta’addancin a Najeriya.
“Shugaban kasa ya ce duk da dai jami’an tsaro na bakin kokarinsu, amma kokarin nasu bai isa ba”, inji Monguno.
Idan ba a manta ba, Shugaban Kasar ya tattauna da Hafsoshin Tsaron kasar ne kwanaki kadan bayan gwamnatin Amurka ta koka a kan kashe-kashen da suke faruwa a Arewacin Najeriya.
Sunan yaki daban-daban, amma salo daya
Binciken da Aminiya ta gudanar ya gano yadda aka sanya wa yake-yaken sojin sunaye daban-daban amma salo da irin kayan yakin suka zamo iri daya babu bambanci, wanda hakan ya haifar da rashin nasararsu.
Wani jami’in tsaro da ke cikin yakin, Ahmed ya ce dole kowane yaki ya kasance an yi masa shiri na daban, “Abun bakin cikin, banda canjin sunan babu wani abu da ke sauyawa”.
Ya ci gaba da cewa ko sau dubu za a sauya sunan yakin ba za a samu galaba ba har sai an yi la’akari da yanayin wuri da matsalolin da ke kasa.
Daya daga cikin sunayen yakin da aka yi a Arewa-maso-Gabas shi ne “Operation Lafiya Dole” da aka kirkira a watan Yuli, 2015 domin kara wa sojoji dubarun yaki da kuma gano ‘yan ta’addan Boko haram.
“A lokacin bukatar Gwamnatin ita ce kawo karshen ta’addanci a yankin da kuma sauran matsalolin tsaro a Kudu-maso-Kudu da saura sassan Najeriya”, inji Ahmed.
A sadda aka kaddamar da yakin, an ruwaito cewar Babba Hafsan Sojin Kasa, Lt Janar Tukur Buratai ya ce, “Wannan yakin Boko Haram an kwashe shekaru ana sauya masa suna kala-kala kafin shekarar 2015.
Bayan shi akwai wani da aka sa wa suna “Sharan Daji”, a Arewa-maso-Yamma domin magance satar shanu da ‘yan bindiga a yankin”.
Duk da hakan, satar shanu na daga cikin manyan matsalolin da ke addabar kasar, ba a Arewa-maso-Yamma ba, har ma da wasu sassan kasar.
Wasu daga cikin sunayen da aka ba yake-yaken sun hada da: “Shirin Harbi”, domin magance rashin zaman lafiya a jihar Gombe; “Harbin Kunama” domin yakar satar shanu a dazuzzukan Zamfara; da “Crocodile smile I”, domin yakar tsagerun Neja Delta masu fasa bututun mai a 2017.
An kuma kirkiri “Harbin Kunama II” a Arewa-maso-Yamma domin magance rikicin manoma da makiyaya da satar shanu; sai kuma “Operation Dokan Daji” a yankin da kuma Arewa ta Tsakiya domin magance rikicin manoma da makiyaya da satar shanu da ‘yan bindiga.
Aminiya ta kuma gano “Operation Egwu Eke” domin yakar kungiyoyin asiri da garkuwa da mutane a yankin Neja-Delta.
Sojojin sun kuma yi “Operation Karamin Goro” a yankunan Minna-Birnin Gwari-Pandogari da Minna-Sarkin Pawa a watan Janairu; da “Operation Ayem Akpatuma” domin yakar kungiyoyin asiri da garkuwa da mutane da ‘yan ta’adda a jihohin Binuwai da Taraba da Kogi da Nasarawa da Kaduna da kuma Naija; hakazalika “Operation Last Hold” da aka aiwatar a Arewacin Borno da yankin Tabkin Chadi a watan Afrailun 2018, domin yakar ‘yan Boko Haram da kuma kwato wadanda suka yi garkuwa da su.
“Operation Egwu Eke (Python Dance II)” kuma, an fara shi ne a watan Augustan 2018, domin magance garkuwa da mutane da fashi da makami da kungiyoyin asiri; sai “Operation 777” domin dakile garkuwa da mutane da fashi sa makami da sauran matsalolin tsaro.
An yi “Operation Egwu Eke (Python Dance) III” a lokacin zaben 2019 domin magance matsalolin tsaro kafin da lokacin da kuma bayan zabe; “Operation Harbin Kunama III” kuma ya kula ne da dazuzzukan jihohin Katsina da Sokoto da Zamfara; sai kuma “Operation Cat Race” domin yakar rashin zaman lafiya da satar shanu da barayin shanu da ‘yan bindiga da sauransu a jihar Neja.
Wani mai suna “Operation Positive Identification” kuma an yi shi ne domin yakar gudaddun ‘yan Boko Haram a Arewa-maso-Gabas cikin watan Nuwambar 2010; akwai kuma “Operation Atilogwu” (Operation Dance for Peace) a Kudu-maso-Gabas.
Sai “Operation Rattle Snake” a wasu tsirarun wurare a Arewa-Maso-Gabas domin kakkabe sauran ‘yan Boko Haram da sojojin “Operation Yancin Tafki’, na hadakar sojojin kasashen Chadi da Nijar da Najeriya domin tarwatsa ‘yan ta’addan da ke Arege da Metele da kuma Duguri.
Wannan ya ba sojin Rukuni na 2 (Chadi) da Rukuni na 3 (Najeriya) damar su hadu da na Rukuni na 4 (Nijar) ta bangaren kogin Komadougou domin yakar ‘yan Boko Haram. Akwai kuma “Operation Long Reach” da aka yi a Arewa-maso-Gabas din.
Har wa yau akwai “Operation Sharan Daji” a Arewa-maso-Yamma, “Operation Whirl Stroke”, a Arewa ta Tsakiya. Bayan su akwai “Exercise Sahel Sanity North West” da “Operation Ruwan Wuta I, II, da na III” a Arewa-maso-Gabas.
Hukumar Sojin Najeriya ta yi Gum
Wakilimu ya tuntubi Kakakin Rundunar Sojin Najeriya, Kanar Sagir Musa, kuma ta tura masa tambayoyin da take son ya amsa a kan sunayen da suka sa na yake-yake daban-daban, da kuma irin cigaba ko cibaya da suka haifar. Amma bai bayar da amsa ba har zuwa lokacin da aka hada wannan rahoto.
Abin da ke hana sojoji samun galaba a yaki
Wasu masana harkokin tsaro sun ce wadannan sunayen da aka sanya wa yake-yaken da ake yi za su magance matsalolin na dan lokaci ne.
A hirar da wakilinmu ya yi da Kabir Adamu ta wayar tarho, ya fada masa cewar wannan salon yakin ana yin su ne na wucin gadi domin kwantar da wata matsalar tsaro.
Adamu wanda masani ne a harkar tsaro ya ce, a Najeriya ana aiwatar da irin wadannan matakan ne na wucin gadi a matsayin hanyoyin gudanar da tsaro na dindindin.
Ya kuma ce, sojin ba su da wata tsawira da suke bi domin gudanar da yakin, ko kuma wata hanya da suke bi na auna nasara ko akasinta a yakin da suke yi.
“Ina da tabbacin duk yakin da suka shiga da maharan babu takamaiman wa’adin lokacin da suke debar wa kansu na dakile ‘yan bindiga ko kuma abin da suke son cimmawa daga karshen yakin” inji shi.
Da ya ke bayani, tsohon Daraktan Fannin Sojoji Masu Amfani da Basira, Manjo Janar Abubakar Sa’ad ya ce tabarbarewar tsarin soja na dubarun yaki ne ya sa suke amfani da salon yakin na wucin gadi.
A cewarsa, “Shekaru da yawa da suka shude, mun daina horarwa da kara bayar da horo da samar da kayan yaki ga jami’an tsaro”.
Sa’ad ya ce jami’an tsaro sun yi watsi da shugabannin addini da na gargajiya wajen amfani da su domin tattara bayannan sirri daga wurinsu.
Ya ce hakan ne ke hana jami’an tsaro samun bayanai a kan kari, wanda ke kara kawo tabarbarewar tsaro a Najeriya.
Ana shi bayanin, Kaftin Sadeeq Shehu, wanda masani ne a harkokin tsaro, cewa ya yi allawadai da yanayin da ake ciki wanda ‘yan ta’adda kan samu galaba a kan jami’an tsaro.
Ya kuma ce hare-haren da sojoji ke kaiwa zai iya kai su ga nasara, sai dai kuma ba sa gudanar da su yadda ya kamata.
Sai dai ya koka cewa nasarar da ‘yan bindiga suka yi a hare-haren da suka kai watanni biyu da suka wuce na da nasaba da rashin jami’an tsaro a yankunan da abun ya faru.
Ya kuma ce akwai matukar amfanin a kore su daga wuraren.”Helikwafta nawa muke da su a Najeriya idan muna son kai sojoji da za su yi yakin da kayan aikinsu a wajen? To, helikwaftoncin da ingantattun kayan aiki ne surrin nasarar yaki” inji Kaftin Shehu