✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda sa’insa kan raken N50 ya kai ga zubar da jini a Kwara

Rikicin ya fara ne lokacin da wani ya sayi raken N50 amma ya ji babu zaki.

A ranar Talata, an shiga yanayin fargaba da hargitsi a kasuwar Mandate da ke Ilorin, babban birnin Jihar Kwara, tsakanin wani mai saye da mai sayar da rake a kan raken N50.

Aminiya ta gano cewa rikicin ya kazance ne lokacin da mutane daban-daban suka rika zaro makamai suna tunkarar juna, lamarin da ya tilasta rufe kasuwar dungurungum.

Kazalika, an garzaya da wadanda suka samu raunuka zuwa asibiti mafi kusa inda suke can suna ci gaba da samun kulawa.

To sai dai wata majiyar ta ce fadan ya fara ne tsakanin daya daga cikin bata-garin da ke gararamba a kewayen kasuwar, kafin ya rikide ya zama tarzoma.

Harkokin kasuwanci dai sun tsaya cik a kasuwar, har zuwa lokacin da ’yan sandan kwantar da tarzoma suka je domin kai dauki a kasuwar.

To sai dai wasu ’yan kasuwar sun bayyana fargabar yiwuwar sake barkewar wani sabon rikicin a nan gaba, matukar ba a yi wa tufkar hanci ba.

Lokacin da wakilinmu ya ziyarci kasuwar, ya iske an girke jami’an ’yan sanda da na sibil defens a kofofin shigarta don kaucewa karya doka.

Da yake tsokaci a kan lamarin, Kakakin hukumar tsaro ta sibil defens a Jihar, Babawale Afolabi, ya ce rikicin ya fara ne lokacin da wani mutum ya sayi raken N50, amma ya dandana ya ji babu zaki.

Ya ce hakan ce ta sa ya bukaci mai sayar da raken ya canza masa, shi kuma ya ki, dalilin da ya sa daga bisani mai sayarwar ya daba masa wuka.