✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda rufe iyakar Kaduna da Plateau ta rutsa manyan motoci

A yayin da gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya bada umarnin, rufe dukkan hanyoyin shiga jihar Kaduna da manyan shingayen siminti, da aka fi…

A yayin da gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya bada umarnin, rufe dukkan hanyoyin shiga jihar Kaduna da manyan shingayen siminti, da aka fi sani da jakin Babangida.

Wannan al’amari ya rutsa da daruruwan manyan motoci, da suka taso daga wurare daban-daban dauke da kayayyakin abinci a kan hanyar  shiga jihar ta Kaduna daga Jihar Filato.

Yadda aka rufe iyakar shiga Kaduna

Direbobin sun bayyana takaicinsu kamar haka:

Wani direban babbar motar tirela da ya taso daga Gombe, mai suna  Abubakar Umar ya shaidawa Aminiya cewa ya dauko dawa ne daga Gombe zai kai Sakkwato, amma ya tarar da hanyar a rufe.

Abubakar Umar, ya ce sun taso tun safiyar ranar Juma’a sai suka samu an rufe iyakar jihar Kaduna babu damar shiga.

“Mun  dauka wannan doka ta hana wucewa bata shafi kayayyakin abinci ba. Amma sai muka samu an garkame iyakar shiga jihar Kaduna, an gindaya ginin siminti, babu wanda zai iya wucewa”.

‘’ A halin da ake ciki mutane suna kulle a ko’ina idan ba a sami abincin da aka kai masu ba, za a dada shiga cikin mawuyacin hali. Don haka muna rokon gwamnati ta dubi wannan al’amari.’’

Direban tankar mai

A cewar wani direban motar tankar daukar mai, mai suna Abubakar Hassan, ya bayyanawa  Aminiya ya bayyana cewa ya kai mai ne Gombe, shi ne yazo ya yi gyara a Jos babban birnin jihar Filato, daga nan ya kama hanyar zuwa Kaduna. Shi ne yazo ya tarar da an garkame iyakar shiga jihar Kaduna.

Ya ce, su sun san duk hanyar da suke bi a kasar nan, ana barinsu suna wucewa, saboda shugaban kasa ya bada izinin da motocin tanki masu daukar mai, da motocin da suke daukar abinci a barsu su wuce.

Abubakar Hassan, ya kara da cewa rufe hanyar  yana shafar masu manyan motoci ne kawai, domin masu kananan motoci suna bin hanyoyin cikin daji su wuce abinsu. Don haka wannan shinge bashi da wata ma’ana.

‘’A samar da kayayyakin aiki na gwaje-gwajen wannan cuta shi ne yafi. A rika gwada mutane kafin su wuce shi ne yafi, amma idan aka ce an sanya wannan shige, masu kananan motoci da suke daukar mutane da yawa, zasu rika wucewa ba tare da an gwada su ba. Masu manyan motoci basa daukar mutane, kuma cutar nan ta mutane ce. Don haka a bar hanyar a bude a rika gwada duk wanda zai fita, shi ne yafi. Amma idan aka ci gaba da tsare manyan motoci, ba za a sami abinci da mai ba.’’

Wasu manyan motocin da suka kwana a gefan hanyar bayan rufe iyakar shiga Kaduna

Direban da ya dauko abincin kaji

Wani direban babban mota da ya dauko kayan abincin kaji, daga Kaduna zai kai Jos mai suna Alhaji Salisu Sai Godiya, cewa ya yi sun taso daga Kaduna ne zasu shiga Jos, sai suka samu an rufe kan iyakar Jihar Kaduna da Filato.

Ya ce, sun dauko abincin kaji ne ana jiransu za a kai gonakin kiwon kaji. Kuma sun yi bayanin haka ga jami’an tsaron da suke aiki a wajen, amma sai suka ce masu umarni aka basu daga gwamnan Jihar Kaduna.

Wakilin Aminiya ya yi kokarin jin ta bakin Kwamishinan tsaro da cikin gida na Jihar Kaduna, Mista Samuel Aruwa domin tuntubarsa kan wannan al’amari ta wayar salula da sakon kar ta kwana, amma ba a samu amsa ba, har ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoto.

Direbobin sun bayyana takaicinsu game da rufe iyakar jihar Kaduna