✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda rudani ya dabaibaye siyasar Kano saboda Zaben 2023

Lissafin siyasar Kano a yanzu kan mutane uku yake.

Yayin da zabukan 2023 ke matsowa, guguwar sauyin sheka a jam’iyyar APC da rashin tabbas ga jam’iyyar PDP na ci gaba da kawo rudani a siyasar Jihar Kano.

Fadi in fada gami da tsallen tsuntsu daga bishiya zuwa bishiya baya ga jifan juna da bakaken kalamai, su ne muhimman batutuwan da a yanzu suka zama gajimaren da ya lullube siyasar jihar Kano.

Yanzu haka dai jam’iyyar APC mai mulkin jihar na cewar galiban masu kaurace mata sun fara yin kome, ungulu tana komawa gidanta na tsamiya.

A hirarsa da Gidan Rediyon Jamsu, Alhaji Ahmed Aruwa, Darektan Yada Labarai na jam’iyyar APC a Kano, ya ce da ma siyasa ta gaji haka kuma jiga-jigan da suka bar jam’iyyar sun fara dawowa har ma ya ce tuni Sanata Barau Jibril na kano ta Arewa ya mayar da wukarsa cikin kube, saboda an daidaita da shi.

Haka kuma ya ce yanzu haka ma suna kokarin sulhuntawa da Sanata Ibrahim Shekarau, wanda shi ma tuni ya nade kayansa domin barin jam’iyya.

Shi ma Honorabul Musa Iliyasu Kwankwaso guda daga cikin na hannun daman gwamna Ganduje, na da ra’ayin cewar da ma siyasa haka ta gada, kuma shi ma ya hakikance da cewar wadanda suka tafi suna kan hanyar dawowa.

Hononorabul Murtala Kore shi ne dan Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar Karamar Hukumar Danbatta kuma guda daga cikin wadanda suka ayyana barin APC amma daga baya suka ce sun daidaita sun dawo, ya ce tangarda aka samu amma yanzu komai ya daidaita.

Daga bangaren magoya baya, masu fashin baki kan siyasa irin su Abubakar Ibrahim na da fasalin cewar lissafin siyasar Kano a yanzu kan mutane uku yake, wadanda su ne shika-shikan fayyace siyasar jihar.

A kowane lokaci daga yanzu za a ji matsayar Malam Ibrahim Shekarau da magoya bayansa, wanda matsayin su ne zai fayyace ainihin alkiblar siyasar Kano a wannan lokaci.

Wannan ne ma ya sa kowane bangare tsakanin Kwankwaso da Ganduje ke kokarin jawo malamin zuwa wurinsu, a waje guda kuma jam’iyyar PDP ta shiga mummunan yanayi na rashin tabbas, kasancewar shugabannin da ke rike da akalarta a yanzu masu imani da akidar tafiyar kwankwasiya ne, lamarin da ke nuna yadda jam’iyyar ke cikin halin kila wa kala.

Kwanaki kadan da suka gabata ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kai ziyarar kamun kafa gidan tsohon gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau, wanda rahotanni ke cewa yana daf da ficewa daga jam’iyyar.

Mai magana da yawun Malam Shekarau Sule Ya’u Sule, ya tabbatar da cewa cikin daren Juma’ar da ta gabata Shekarau ya karbi bakuncin Ganduje, wanda ya je da zummar lallashi da kuma sauya wa Shekarau ra’ayi.

Ko da yake kakakin tsohon gwamnan ya ce basu san me mutanen biyu suka tattauna ba, saboda haka ba za a iya hakikance ko Shekarau zai amince da sulhu da bangaren Ganduje ko ba zai amince ba a wannan lokaci.

A bayan nan dai rikici ya yi kamari tsakanin Malam Ibrahim Shekarau da Ganduje kan jagorancin jam’iyyar APC a Jihar Kano, lamarin da ya kai ga har Kotun Koli, daga bisani aka tabbatar da shugabancin jam’iyyar na bangaren Ganduje a matsayin halastacce.

An yi ta yada rahotannin cewa tsohon gwamnan na Kano, Shekarau zai sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP ta Rabiu Musa Kwankwaso, kodayake Shekarau din bai bayyana haka da bakinsa ba.

Wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da dama a Kano kamar tsohon mai ba wa shugaba Muhammadu Buhari shawara kan harkokin siyasa Kawu Sumaila, da tsohon shugaban Majalisar Dokokin jihar Kabiru Alhassan Rurum da wasu ‘yan majalisar dokokin jihar kusan 13 da na wakilai sun sauya sheka zuwa jam’iyyar ta NNPP ta Kwankwaso.