✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda rikicin ’yan bindigar Binuwai ya ki karewa

Jami’an tsaro na aiki ba dare ba rana don su tsare rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Binuwai.

Zubar da jini a kauyen Gbagir

Karar abubuwa irin na manyan bindigogi masu aman wuta da ke jefa tsoro ya kaure a kauyen Gbagir da ke Karamar Hukumar Ukum ta Jihar Binuwai.

Wannan shi ne fada na bayabayan nan na neman nuna karfin iko da ake yi a tsakanin kungiyoyin matasa ’yan bindiga da ake kira ‘Full Fire’ da abokan karawarsu da ake kira ‘Chain’ da sauran ’yan bindiga a kan iyakar Zaki Biyam da ke (Jihar Binuwai) da Wukari da ke (Jihar Taraba) a rikicin da ya barke a ranar 5 ga Maris din bana (2024).

Wannan karar harbe-harben ya firgita al’ummar yankin har ya sa suka rika tunawa da fadan da aka yi ta yi lokacin marigayi Terwase Akwaza (Gana).

Da dama daga cikin mazauna yankin da ba su ji ba, ba su gani ba, akasari mata masu rauni da yara da tsofaffi, suka yi ta gudun tsira da rayukansu, inda da yawa daga cikinsu suka samu munanan raunuka a kokarin tserewa daga yankin don su tsira da ransu.

A kidaya ta karshe da aka yi bayan kura ta lafa, sama da rayuka 40 da suka hada da ’yan uwa bakwai, suka rasa rayukansu a zubar da jinin da ya faru, inda kuma aka kone gidaje da dama.

Ko da yake akasarin wadanda harin ya rutsa da su ’yan kungiyoyin ’yan bindiga ne daban- daban da ke fada da juna, amma an kashe manoma 12 da ba su ji ba, ba su gani ba a cikin garin, a wata arangama da aka yi yayin da wasu mutanen kauyen 30 suka samu raunuka.

Bincike ya nuna cewa rikicin da ya barke a Gbagir ramuwar gayya ce bayan da wani jagoran ’yan bindiga a Karamar Hukumar Ukum ta Jihar Binuwai ya yi garkuwa da takwaransa na al’ummar Chinkai a Karamar Hukumar Wukari ta Jihar Taraba.

Wanda aka kashe, mai suna Alhaji Ghana, wanda aka yi garkuwa da shi tare da iyalansa, an ce ya shahara da yin fashi da kuma garkuwa da mutane.

An nemi kudin fansa Naira miliyan 100, amma an gano cewa daga baya an biya Naira miliyan 5 domin a kwato su.

Sai dai kuma bayan karbar kudin, an ce ’yan bindigar da suka fito daga garin Ukum sun kashe mutanen da suka yi garkuwa da su, lamarin da fusata ’ya’yan kungiyar wadanda aka kashe, suka yi gaggawar daukar matakin ramuwar gayya.

Rikicin neman iko

Wani abin mamaki, a ranar Asabar din makon jiya, Aminiya ta samu labarin cewa, bayan kashe wadanda aka yi garkuwa da su da suka fito daga Taraba, wani shugaban ’yan bindigar da ke neman nuna iko daga Karamar Hukumar Ukum ta Jihar Binuwai ya hada baki da abokan fadansu a wani mataki na ramuwar gayya domin kawar da ’yan kungiyar da ke adawa da kauyensa.

Manufar haka, kamar yadda bincike ya nuna, ita ce don ya samu damar zama shugaban ’yan bindiga a yankin Ukum.

A farkon watan Janairun bana, akalla mutum 9 aka kashe a wani hari da wasu ’yan bindiga suka kai a kauyukan Mbatyula da Mbayongo a Karamar Hukumar Katsina-Ala ta Jihar Binuwai.

A cikin kwana uku da aka kwashe ana tafka kazamin fada, wanda ke da alaka da rikicin nuna karfin iko, an ce an kone gidaje da dama daga bangaren ’yan bindigar.

Wani mazaunin Katsina-Ala da ya tuno da faruwar lamarin ya ce, “Shiryayyun hare-hare ne da wasu ’yan bindiga da ake zargin daga kauyen Mbayongo suka kai a wasu yankunan mazabar Mbatyula.

“A waccan ranar, ’yan bindigar sun kai farmaki Atumbe, wata unguwa a kauyen Mbatyula, inda suka kone gidaje tare da kwashe wasu kadarori.

“Daga baya sun koma Kur Hile, wata unguwa a kauyen Mbatyula, inda nan ma suka kone wasu gidajen.

“Haka lamarin ya faru a Unguwar Anyom a kauyen Mbatyula a ranar Laraba 17 ga Junairun 2024, inda aka kashe mutum bakwai tare da kone gidaje da dama suka zama toka,” in ji shi.

Shugaban Riko na Karamar Hukumar Katsina-Ala, Mista Zamzam Francis ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma an ruwaito shi yana cewa fada ne a tsakanin ’ya’yan kungiyoyin ’yan bindigar da ke gaba da juna ya haifar da haka.

Sannan a cikin watan Maris din bana, wani abin takaicin ya sake aukuwa a kan hanyar Wukari zuwa Takum a Jihar Taraba, inda ake zargin wasu ’yan bindiga daga yankin Ukum na Jihar Binuwai, sun far wa wasu mutanen yankin da ke kan hanyarsu ta zuwa aikin bisharar addinin Kirista na shekarashekara a Takum.

“Sun yi wa mutanenmu kwanton-bauna a hanyar Wukari, ana cikin haka ne suka kashe mutum uku tare da kwace motarsu yayin da wasu hudu suka samu raunuka kuma aka kwantar da su a Babban Asibitin Wukari,” in ji wani Shugaban Matasa a Wukari.

Majiyar wadda ba ta so a bayyana sunanta saboda dalilai na tsaro ta ce: “Wadanda suka aikata ta’asar ’yan bindiga ne daga yankin Sankera na Jihar Binuwai da ke jin dadin yin garkuwa da su domin tara kudade da kuma biyan bukatunsu na zubar da jini.

“Sun kasance suna yi mana haka a irin wannan lokaci na bukukuwa a kowace shekara. Mun yi hakuri mun gaya wa yaranmu kada su rama. Amma idan suka ci gaba, za a tilasta mana mayar da martani.”

Yadda ’yan bindigar Binuwai suka faro suka watsu Binciken da Aminiya ta gudanar ya nuna yadda wasu gungun ’yan bindiga suka ci gaba da zubar da jini a kan iyakar jihohin Binuwai da Taraba kafin shekarar 2001, inda aka zargi matasa ’yan kabilar Tibi da yin garkuwa da sojoji 19 tare da kashe su.

Hakan ya biyo bayan wasu hare-hare da kungiyoyin Tibi da Jukun suka kai a Jihar Taraba, da kuma yankunan da ke kan iyakar jihohin biyu.

Sojojin, a cewar hukumomin gwamnati, sun yi wani aiki ne na maido da zaman lafiya a yankin da rikicin da aka dade ana gwabzawa a tsakanin kungiyoyin da ke fada da juna ya shafa.

Sai wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a kauyen Baase a Jihar Binuwai a ranar 10 ga watan Oktoban 2001, inda aka gano gawarwakinsu daga baya.

Bayan kwana biyu, a ranar 12 ga watan Oktoban 2002, a harabar makarantar firamare a garin Zaki-Biyam, sojoji sun kai wani mummunan harin ramuwar gayya a Zaki-Biyam da sauran wurare.

Bayan kisan kiyashi a ZakiBiyam, an ce ragowar matasa ’yan bindiga na kabilar Tibi sun haukace suka fara ta’addanci, har suka fada hannun ’yan siyasa musamman a yankin Sankera da ya kunshi kananan hukumomin Katsina-Ala, Ukum da Logo.

“Ayyukan ta’asa na ’yan bindigar sun dauki sabon salo a yankin Sankera na Jihar Binuwai a lokacin da ’yan siyasa suka fara amfani da ragowar matasan kabilar Tibi bayan faruwar lamarin ZakiBiyam a shekarar 2001, don kafa kungiyarsu ta ’yan bangar siyasa,” in ji wani babban dan siyasa daga Katsina-Ala.

Majiyar wadda ba ta so a bayyana sunanta saboda dalilai na tsaro ta ce: “Dukkan manyan ’yan siyasa daga yankin sun fara kafawa da samar da makamai ga matasan ’yan bindigarsu, wadanda aka yi amfani da su a lokacin zabubbukan 2019 da zabubbukan da suka biyo baya.

Bayyanar ‘Yaran Gana’

A kusa da karshen wa’adin farko na mulkin tsohon Gwamnan Binuwai, Gabriel Suswam ne, aka kaddamar da wata kungiyar matasa a wani taron da aka yi a Katsina-Ala.

Kungiyar wadda ta kasance kamar kungiyar ’yan banga ce a farkon kafa ta, an dora mata alhakin kare yankin Sankera daga hari daga wajen yankin, kuma kungiyar ’yan bangar ta kasance a karkashin jagorancin marigayi Terwase Akwaza, wanda aka fi sani da Gana.

Ko da yake an ce ta fara gudanar da aiki bisa tsarin da aka ba ta da farko, amma nan da nan Gana da yaransa suka fara shiga cikin ayyukan da ake zarginsu da aikatawa, kamar fashi da makami da satar shanu.

Yunkurin da gwamnatin jihar ta yi na dakatar da kungiyar ya yi matukar wahala domin kamar yadda wata majiya ta ce: “Yaran sun samu sana’a mai tsoka.”

Ana kyautata zaton Gana ne kanwa uwar-gami a kan rikicin da ya barke a tsakanin al’ummomin kan iyakar Binuwai da Taraba, wanda ya kai ga kashe mutane da dama da kuma barnata dukiya ta biliyoyin Naira a bangarorin biyu.

An kuma yi imani cewa shi ne babban mai sace-sacen jama’a a jihohin Taraba da Binuwai, ciki har da ’yan uwansa ’yan kabilar Tibi wadanda suka sha muguwar wahala kan miyagun ayyukansa.

“Shigar da ayarin tsaron hadin gwiwa na ‘Operation Zenda’ domin dakile ta’asar Gana da yaransa bai haifar da wani sakamako ba ko kadan, inda suka koma cikin daji, suna shiryawa tare da aiwatar da hare-hare da sace-sacen mutane lokaci-lokaci,” kamar yadda wata majiyar tsaro ta shaida wa Aminiya.

Shirin afuwar Ortom

Lokacin da tsohon Gwamna Samuel Ortom ya gaji Gibrael Susuwan sai ya bullo da shirin yin afuwa saboda a kawo karshen batun Gana.

A shekarar 2015 aka fara yin afuwar wadda Gana ya zama wanda ya fi kowa cin moriyar shirin.

A karshen ranar da aka yi masa afuwar ya mika bindigogi sama da 84 da dubban albarusai.

Haka ba kawai afuwar aka yi masa ba, har ila yau Gwamnatin Jihar ta ba shi mukamin mai kula da harkar harajin jihar domin kokarin sake inganta rayuwarsa.

Sai dai ba a dade da yin wannan afuwar ba wani abu ya auku wanda ya lalata dukkan al’amura.

Majiyarmu ta shaida mana cewa bayan da al’amarin ya faru ya sake daukar nauyin kisan gillar da aka yi wa Babban Mashawarcin Gwamnan a kan Tsaro Mista Denen Igbana.

“Daga baya, Gana ya dora biyan wasu kudade a kan manoma da ’yan kasuwa da mutanen gari a yankin da yake, idan mutum ya ki biya kuma to a bakin ransa.

Ya yi fada da dukkan abokansa wadanda suke ziyartar al’ummomi dabandaban a kananan hukumomin Katsina Ala da Ukum.

“Wannan hali da aka shiga shi ya sa manyan sanannun ’yan asalin jihar da suke yankunan da suka hada da shugabannin siyasa da na addini da na gargajiya suka nemi a sake dawo da shirin yin afuwa daga gwamnati, musamman ganin cewa sojoji sun gaza kama shi,” inji wani shugaban al’umma da ya nemi a boye sunansa.

A ranar Jumaa 4 ga Satumban 2020 a wani zagayen aiki da Gwamna Ortom ya kai yankin Sankera, sai ya yi na’am da rokonsu.

Sai ya ba wadanda ke son afuwar a karo na biyu wa’adin su mika makamansu zuwa ranar 8 ga Satumban 2020.

Kafin cikar wannan wa’adi al’ummar Sankera sun shawo kan dukkan masu dauke da miyagun makamai su mika su ga hukuma.

Ta haka ne Gana ya samu afuwa a karo na biyu. Majiyarmu ta ce a bisa rakiyar shugabanin addini Gana ya fito daga maboyarsa ya bayyana kansa a filin wasa na Emmanuel Akume da ke Katsina-Ala a gaban mutane ya karbi wannan afuwa ta gwamnati.

A daidai wannan lokaci jami’an tsaro a jihar suna gudanar da taron koli a kan abin da ya shafi tsaron jihar a dakin taro na Gidan Gwamnatin Jihar.

Wasu zababbun shugabannin al’umma da wasu sanannun mutane da jami’an tsaro da ’yan siyasa sun tafi da Gana zuwa Makurdi inda ake gudanar da taron koli kan tsaron.

Tun kafin ya bar garinsa, Gana ya shirya wa sojojinsa domin yana zargin cewa ana shirin yi masa kofar rago don haka ya gaya musu cewa ko da ta kasance bai dawo ba, to, su ci gaba daga inda ya tsaya.

A kan hanyarsu ta zuwa Makurdi ne sojoji suka hargitsa jerin gwanon motocin a garin Masaje kusa da Yandeb a Karamar Hukumar Gboko inda aka kashe shi.

Gibin da Gana ya bari da rikicin hawa kujerarsa

Bincike ya nuna cewa bayan rasuwar Gana abubuwa sun fara lalacewa a tsarin shugabancin tawagarsa.

An san cewa Gana ya yi kokari wajen kula da sojojinsa da ke jihohin Binuwai da Taraba. Shi mutum ne da ya yi kokarin samun cikakken ikon komai.

Baya ga fashi da garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuffuka, Gana ya yi kkoarin dora wa ’yan siyasar da suke amfanuwa da shi daukar nauyin mutanensa.

Sai dai ba haka al’amarin ya kasance ba bayan mutuwarsa, domin an shiga tsaka-mai-wuya wajen samun kudin gudanarwa a gefe guda kuma ga rigimar shugabanci a tsakanin sojojinsa da kuma sababbin kwamandojinsu.

“Tun daga wannan lokaci aka rasa shugabanci na baidaya, inda aka wayi gari kowane bangare yana kokarin ya ci gashin kansa.

“Ba kamar Gana da yake samo kudinsa daga ’yan siyasa ba sai ya kasance su sababbin kwamandojin ba su samun wannan taimakon kudi, wasu daga cikinsu sai suka koma bin Fulani makiyaya da ke Kwande da Guma don su karbi kudi a hannunsu, inda suka yi musu alkawarin samun burtalin da za su zauna don yin kiwo ba tare da samun matsala ba a cikin al’ummominsu.

“Makiyayan sai suka rika jin cewa an sayar musu da wurin, lamarin da ya janyo tashe-tashen hankula a tsakanin makiyaya da manoma.

’Yan siyasa sun yi amfani da su sun watsar

Aminiya ta gano cewa babban abin da ya janyo yawaitar ’yan bindiga a yankin Sankera a Jihar Binuwai shi ne ’yan siyasa sun yi amfani da su sun kuma watsar da su.

A karshe-karshen mulkin Ortom ’yan siyasar da ke neman mukamai daban-daban sun yi amfani da kungiyoyin ’yan bindiga inda suka yi musu alkawura masu yawa ciki har da batun afuwa.

Baya ga samar da kariya ga ’yan siyasa a lokacin yakin neman zabe, wasu daga cikin wadannan mutane sun bayar da gudunmawar kudi a lokacin zaben wasu ’yan siyasa a yankunansu.

A lokacin yakin neman zabe Gwamnan Jihar Binuwai na yanzu Rabaran Hycinc Alia ya yi alkawarin samar da cikakkiyar afuwa ga tubabbun ’yan bindigar.

Lokacin da yake bayani game da ayyukan da zai yi idan ya ci zabe, Gwamnan ya yi alkawarin samar da motoci ga jami’an tsaro a dukkan shingayen bincike musamamn a wuraren da suka yi kaurin suna wajen fashi da garkuwa da mutane da sauransu.

Wani malami a Tsangayar Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Jihar Binuwai ya danganta yawaitar ’yan bindigar a jihar da irin kin cika alkawuran ’yan siyasa wadanda ya ce sun yi amfani da su tare da watsar da su a lokacin guda, ya ce, “Bayan zabe ’yan siyasa wadanda suka yi amfani da irin wadanan gurbatattun yara sun ki cika musu alkawuran da suka yi musu musamman batun masu afuwa daga gwamnati.

“Kada ka yi tsammanin yaran da ke da makamai za su zauna su zura ido suna kallon ’yan siyasa suna wadaka da jin dadi yayin da su kuma suke cikin wahala.”

‘Abin da gwamnatin Binuwai take yi a kai’

Yayin da yake amsa tambaya a kan alkawarin da Gwamnan ya yi a lokacin yakin neman zabe kan batun yin afuwa ga tubabbun ’yan bindigar, Mai taimaka wa Gwamnan a Harkar Yada Labarai, Mista Solomon Lorpeb ya shaida wa Aminiya cewa wannan alkawari yana nan daram ga duk wanda yake so ya bar harkar ta’addanci don ya sake samun ingantacciyar rayuwa don ci gabansa da na iyalinsa da al’ummarsa da kuma Jihar Binuwai baki daya.

Mista Solomon Lorpeb ya ce kofar Gwamnan a bude take ga duk wanda ke son canjin rayuwa da ci gaba, kan ya fito fili ya taimaka masa wajen gina sabuwar Jihar Binuwai.

“Akwai damarmaki masu yawa a shriye-shiryen da Gwamnan ke son aiwatarwa muna fata za su yi amfani da wannan dama wajen inganta rayuwarsu tare da jihar gaba daya.

“Kada ka mance dama shi mai wa’azi ne da ke dawo da mutane kan hanya, don su yi ingantacciyar rayuwa haka kuma yana wa’azi a kan su zauna lafiya da juna, saboda haka dawo da wasu da suka fandare zuwa kan hanya madaidaiciya ba wani bababn aiki ba ne a wurinsa,” in ji shi.

Game da batun matakin da gwamnatin ta dauka don magance matsalolin tsaro a jihar musamman abin da ya shafi harkar ’yan bindiga da tashe-tashen hankula a tsakanin manoma da makiyaya, Kakakin Gwamnan ya ce duba da cewa Gwamnan ya damu da jin dadin mutanensa, yana kokari ba dare ba rana wajen ganin ya samar da cikakken tsaro a gare su.

“Yana shiga ana tattaunawa tare da masu ruwa-da-tsaki don magance matsalar rashin tsaro a jihar.

“Hakan ya sa muka dan samu tsaro a yanzu. An baza jami’an tsaro a kusan dukkan wuraren da ake da rashin tsaro don a dakile duk tashintashinar da ka iya tasowa.

“Haka ya kaddamar da sassan tsaro don su yi maganin duk wata tarzoma da ka iya tasowa kamar su Mini-Marshal da Agro Rangers da sauransu.

“Duk da cewa yawancin rashin tsaron da ake samu ya samo asali ne kafin zuwan wannan gwamnati, amma hakan bai hana gwamnatin daukar matakin da ya kamata don samar da tsaro ba, inda jami’an tsaro ke aiki ba dare ba rana don su tsare rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Binuwai.