’Yan’uwa da abokan arziki suna ta yin turuwa zuwa asibitin kwararru na Yola don jajantawa al’ummar fulani da harin baya-bayan nan ya rutsa da su a cikin garin Numan da ke jihar Adamawa.
Ma’aikatan lafiya na yin kokari don ceto rayukan mutum 32 mata da kananan yara wadanda suka sami munanan raunuka wanda ake zargin ’yan kabilar Bachama suka kai.
Kimanin mutum 55 aka ruwaito sun mutu amma shugabannin al’ummar sun ce ana samun karuwar gawarwakin wadanda aka kashe.
An ce an kai harin na kauyen Kiken da wasu kauyuka a da yammacin ranar litinin din da ta gabata yayin da mazan kauyukan ba sa nan.