✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda Rikadawa ya martaba yaronsa da auren ’yar cikinsa

’Yan Kannywood sun yi dandazo don shaida daurin auren ’yar Rikadawa da angonta.

Jarumin fina-finan Hausa na Kannywood, Rabiu Rikadawa ya aurar da ’yar cikinsa mai suna Fatima ga babban yaronsa a harkar fim mai suna Salisu Abdullahi (Babangida).

Rikadawa cikin farin ciki ya garzaya shafinsa na Instagram yana bayyana murnarsa da ganin daurin auren Fatima da angon nata wanda suka jima suna soyayya.

“Daurin auren ’yata Fatima Rabiu Rikadawa! Na gode Allah ina farin ciki da ganin wannan rana mai cike da tarihi a rayuwata,” inji uban amarya.

Juma’a daga ciki da wajen Kannywod da suka hada da Adam A. Zango, Yusif Saseen, Alhassan Kwalli, Sani Musa Danja da sauransu sun halarci daurin auren da ya gudana a Babban Masallacin Juma’a da ke unguwar Kabala a Jihar Kaduna.

Adam Zango tare da Rikadawa a wajen auren Fatima Rikadawa da Babangida.

Ango Salisu ya shaida wa Aminiya cewa “Mun jima ni da Fatima muna soyayya kuma maigida ya sani, ya kuma yi mana fatan alheri.

“Soyayyarmu ta yi karfi sosai, ga shi har ta kai mu ga yin aure,” inji ango Babangida, jarumi kuma mai shirya fina-finan Hausa.

Jarumai maza da mata, masu shiryawa da ba da umarni a Kannywood sun yi ta zuwa shafukansu na Instagram suna taya Rikadawa da kuma ango da amarya murnar auren da aka shafa Fatiha ranar Juma’a 5 ga Fabrairu, 2021

Sani Danja a wajen daurin auren ‘yar Rikadawa, Fatima.

Daga cikinsu akwai Aminu Saira, El-Mu’az, Nasir Ali Koki, Ali Nuhu, Kamal S. Alkali, Abubakar Bashir Maishadda, Rahama Sadau, Hadiza Gabon, Saratu Gidado, Yakubu Mohammed, Abba El-Mustapha, Baballe Hayatu, Ali Jita, Nura M. Inuwa, Ado Gwanja, Umar M. Shariff da sauransu.