Noman citta da kasuwancinta da gyaranta na daga cikin harkoki mafiya girma da ke bunkasa harkokin arziki da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin al’ummar Kudancin Kaduna, yankin da ya fi ko’ina yawan tashin hankali a fadin Jihar.
Cittar da ake nomawa a Kudancin Kaduna, wadda kuma aka yi amanna tana daga cikin mafiya kyau a duniya, akan fara girbinta ne daga watan Nuwamba a shekara zuwa watan Afrilun shekara ta gaba.
A lokacin da ake ganiyar aikin cittar, mutane da dama da suka hada da manya da kananan ’yan kasuwa da dillalai da direbobi da masu dako da masu gadi da masu aikin tsinta da shika da gyaran cittar, kowanne kan kama aiki gadan-gadan, baya ga manomanta da ke fitowa da ita domin sayarwa a kasuwa.
Matasa, yara, maza da mata na cin gajiyar noman citta
Matasa maza da mata da kananan yara na daga cikin wadanda suke cin gajiyar aikin da ya karade ciki da wajen garin Kafanchan a Karamar Hukumar Jama’a da kuma garin Kachiya na Karamar Hukumar Kachiya, dukkansu a yankin Kudancin Jihar Kaduna.
Baya ga mazauna kuma haifaffun garuruwan, akwai masu aikin cittar da musamman suke baro garuruwansu su taho yankin don aikin gyaran citta a kowace shekara.
Kasuwancin citta daga Kafanchan zuwa sassan Najeriya da kasashen ketare
Mutane daga jihohin Sakkwato da Zamfara da Jigawa da Kano da Katsina da Arewacin Jihar Kaduna kan zo Kudancin Jihar don yin wannan aiki na gyaran citta.
Garuruwan Maraban Walijo da Gidan Mana (Boda) da ke Karamar Hukumar Kachiya da Kagarko da Kubacha da ke Karamar Hukumar Kagarko da Barde da Fori da ke Karamar Hukumar Jama’a, sai Kwoi da ke Karamar Hukumar Jaba; su ne manyan garuruwan da ke samar da kashi mafi yawa na noman citta ba kawai a Jihar Kaduna ba, hatta a fadin Najeriya baki daya, inda nan ne ake zuwa a sayo a kawo su Kafanchan, wajen ya zama matattarar aiki da gyaran cittar da kuma kasuwancinta zuwa jihohin Legas da Borno da Adamawa da Kano da sauran jihohi da ma kasashen waje.
Yadda ake aikin gyara da safarar citta a Kafanchan
A kowane mako, tireloli 15 zuwa sama ne ke daukar citta a Kafanchan, inda kowacce ke daukar tan 26-28, wato buhu 700 zuwa 725, a lokacin da ake ganiyar aikinta.
Wata mai aikin gyaran citta a Kafanchan mai suna Patient Dabid, wadda ta ce ta fara aikin gyaran citta da ya kunshi cire tsakuwa da duwatsu da kashin dabbobi da ciyayi da kuma cire danyu daga cikin busassu ne a shekarar 2016.
“Da farko nakan rako mahaifiyata ce da ke wannan aiki tun ina karama. A lokacin da na gama karatun sakandare sai ni ma na kama aikin gadan-gadan. Na fara ne da gyara buhu hudu a ranar farko amma a yanzu ina iya gyara buhu 30, inda ake biyanmu Naira 100 a kan kowane buhu,” inji ta.
Patient, mai kimanin shekara 30 ta ce da wannan aiki ne take daukar nauyin mahaifiyarta da ta manyanta a yanzu kuma da shi ne take daukar nauyin karatun ’ya’yanta biyu inda a halin yanzu ta yi wa babbar rajista a aji daya na karamar sakandare. “Kuma ina amfani da abin da na samu wajen noman wake da doya a kauyenmu da ke Manchok a Karamar Hukumar Kaura a Jihar Kaduna.
“Akwai wata kawata da ke tuyar kosai wadda bashi ya yi wa katutu, ni na ba ta shawarar ta zo ta kama aikin citta. In takaita maka, yanzu ta biya dukkan basussukan da ke kanta. Hikimar da ta yi ita ce, idan ta gama aikin citta zuwa rana da yamma kuma sai ta koma tuyar kosai. Ni ma, a halin yanzu ma’aikaciya ce a Asibitin Throneroom da ke nan Kafanchan amma duk da haka ina amfani da lokutan canjin aiki in zo in yi aikin citta saboda rufin asirin da ke ciki.”
Ita kuwa Cecelia Ishaku, wadda aka fi sani da Maman Baby, wacce ta ce ta kwashe fiye da shekara ashirin tana aikin cittar, ta shaida wa Aminiya cewa tana aikin ne tun lokacin da ake biyansu Naira 15 zuwa 20 a kowane buhu. “Amma yanzu ana biyanmu Naira 80 zuwa Naira 100 a kowane buhu. Na mallaki komai nawa ne kama daga abinci da tufafi da komai ta hanyar wannan aiki. Har gida na gina kuma da aikin nake daukar nauyin karatun ’ya’yana, inda babbansu a yanzu haka ya kammala karatun a Kwalejin Ilmi ta Jihar Kaduna da ke Gidan Waya a Kafanchan, har ya fara aikin koyarwa,” inji ta.
Ta ce a baya takan yi aikin buhu 40 a kowace rana amma yanzu saboda leburori sun yi yawa ciki har da matan aure, hakan ya sa buhu 25 kawai take samu. “Amma duk da haka babu laifi,” inji ta.
Ita kuwa Maryam Abdullahi, wata matar aure da ta shafe shekara hudu tana sana’ar sayen buhunan kurar citta bayan an tsince manya da kanana an tankade, ta saya domin sayar wa ’yan koli, wadanda suke yin yaji da ita ta ce tana samun alheri a ciki sosai.
Matasa ‘yan makaranta na aikin su dauki nauyin karatunsu.
Ladan Shamsuddeen, wani matashi da ya kammala karatun NCE, ya ce da aikin citta ne ya dauki nauyin karatun da ya yi. “Na fara ne a matsayin mai sa ido ina duba yadda masu tsinta da shika suke gudanar da aikinsu a shekarar 2000 amma yanzu ina rakiyar tirela ce zuwa Legas bayan an loda mata citta tun daga shekarar 2015,” inji shi.
Ya ce da wannan aikin yake daukar nauyin ’ya’yansa biyu tare da taimaka wa ’ya’yan ’yan uwa. “Don haka zan yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga matasa ’yan uwana, musamman wadanda suka kammala karatun kwaleji ko jami’a su tashi su kama sana’a ko wani aikin, kada su tsaya bata lokacinsu wajen jiran aikin gwamnati,” inji shi.
Yahaya Umar, wani dan ci-rani ne da ke zuwa daga Jihar Sakkwato kowace shekara, ya ce yana hada aikin cittar ce da sayar da kaya da yake yi a shago. “Nakan sayi citta daga masu kawowa a kwanon kaya ko a leda ina tarawa har in cika buhu. Daga nan sai in sayar wa dillalan cittar, abin da na samu sai in kasa a shago sauran kuma in kara sayen wata cittar ina ci gaba da sayarwa.
Shi kuma wani saurayi dan kimanin shekara 15 mai suna Haruna Amir Magaji, wanda yake aji shida a makarantar firamare, ya ce yana zuwa aikin cittar ce a ranakun karshen mako ko lokutan hutu. “Na fara koyon aikin ne tun ina dan shekara 11, lokacin nakan samu Naira 200 zuwa 500 amma yanzu nakan samu Naira dubu biyu zuwa uku a kowace ranar aiki,” inji shi. Ya ce yana amfani da abin da yake samu ta hanyar gyaran cittar da ya hada da durawa a buhu da dinkewa da lodawa a mota, ya sayi kayan karatu da tufafi kuma yakan taimaki kannensa kuma ya yi tari don biyan wasu bukatun.
A baya can lokacin da Najeriya ba ta rufe kan iyakokin kasarta na kan tudu ba, ana safarar citta daga kasar zuwa kasashen Binnin da Ghana da Togo wadanda suka yi iyaka da kasar daga Kudu maso Yamma, kana masu harkar cittar zuwa wannan yanki sun tabka gagarumar asara a daidai lokacin da kasar ta rufe iyakokinta na kan tudu lamarin da ya rutsa da tarin manyan motoci dauke da danyar citta wadanda aka hana su yin gaba ko baya.