Ya zuwa yanzu an shafe makonni ana fuskantar karancin man fetur tare da rashin wutar lantarki, lamarin da ya illata kananan ‘yan kasuwa da dama a fadin Najeriya.
Wasu kasuwancin sun rufe na dan wani lokaci, yayin da wasu suka rage sa’o’in aiki don shawo kan karancin makamashi.
Hukumomin kasar dai sun dora alhakin karancin man fetur din ne a kan lamarin gurbataccen man da ya kai kimanin lita miliyan 170 da aka shigo da su daga Turai a watan Janairu.
A watan Fabrairu, gwamnati ta ba da sanarwar cewa ta fitar da lita biliyan daya na man fetur daga asusun ajiyar kasar don daidaita rarrabawa.
Sai dai a yayin da ake samun hauhawar farashin mai da iskar gas a duniya, lamarin dai na ta tafiyar hawainiya kuma yana shafar tattalin arzikin kasa baki daya.
A wannan makon ne Hukumar Kididdiga ta Najeriya ta ce hauhawar farashin kayayyaki a kasar ya karu zuwa kashi 15.7 a shekara.
“Lamarin na neman ya zame ruwan dare,” in ji wani mazaunin Abuja kuma direba mai suna, Mohammed Enesi.
Najeriya ita ce kasa mafi arzikin man fetur a Afirka, amma tana kan fama da biyan bukatunta na makamashi.
Kimanin kashi 47 cikin 100 ne na ‘yan Najeriya ke samun wutar lantarki idan har akwai, kamar yadda kiyasin bankin duniya ya nuna. Hukumomin Najeriya a shekarar 2020 sun rattaba hannu kan yarjejeniyar wutar lantarki da takwarorinsu na Jamus domin inganta samar da wutar lantarki.
Sai dai masana sun ce karancin makamashi na illa ga ‘yan kasar.
“Har yanzu ba mu sami damar daidaita yanayin ba,” in ji manazarci Rotimi Olawale. “A gaskiya a cikin shekaru biyun da suka gabata ba mu ga irin wannan karancin man fetur da muke gani a yanzu ba.
A cikin makon nan ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wa ‘yan kasar alkawari cewa nan ba da jimawa ba za a kawo karshen matsalar man fetur da wutar lantarki.
Amma har sai lamarin ya daidaita, miliyoyin mutane da kasuwani za su ci gaba da shan wahala.
Muna aiki tukuru don inganta wutar lantarki —Gwamnati
Gwamnatin Tarayya ta ce an samu nasarar maido da wutar lantarki bayan katsewarta a farkon makon nan, lamarin da ya jefa kasar cikin duhu, sakamamon karancin gas da kuma ayyukan masu fasa bututun da ke samar da gas ga manyan tashoshin samar da wutar lantarki.
Sanarwa da ke dauke da sa hannun Ministan Lantarki Injiniya Abubakar D. Aliyu da aka fitar ranar Asabar ta kara da cewa, an samu nasarar gyara bututan gas da aka lalata a babbar tashar lantarki ta Okpai, wanda hakan ya samar karin wutar lantarki da ake samu.
Ministan ya kuma kara da cewa, ana daf da kammala gyaran dukkan rashohin wutar lantarki da suka dakatar da aiki sakamakon gyarasu da aka saba yi daga lokaci zuwa lokaci.
Sanarwar ta kara da cewa, an amince akan sabon tsari da farashin gas da za a rika baiwa kamfanoni da suke da tashoshin samar da wutar lantarki, ta yadda zasu ci gaba da aiki ba tare da bata lokaci ba.
Injiniya Abubakar Aliyu yace, gwamnati ta shi tsaye wajen ganin an magance dukkan matsalolin da suke kawo koma baya ga harkar wutar lantarki da suka hada da; karancin gas, fasa bututan gas da kuma gyara wasu tashohin lantarki.
Cikin sanarwar ministan ya bayyana cewa tun daga ranar 14 ga wannan watan masu ruwa da tsaki suke ci gaba da aiki tukuru domin ganin cewa irin wannan matsala bata sake faruwa ba.
Ministan ya kuma ce ana aiwatar da sabbin matakan da aka amince da su domin hana sake aukuwar wannan matsala, yana mai tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa, kokarin inganta samar da wutar lantarki da gwamnati take yi zai ci gaba.