Fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya jawo cece-kuce musamman a kafofin sada zumunta, inda mutane suke ta musayar yawu.
Aminiya ta ruwaito Rarara a makon jiya, inda ya bukaci duk masoyin Shugba Muhammadu Buhari ya tura masa Naira dubu daya domin fitar da sabuwar wakarsa.
A cewarsa, wakar za ta kunshi ayyukan da shugaban ya yi guda 92 da zai yin bayaninsu a cikin a wakar domin nuna wa duniya cewa Buharin na aiki.
Ya kara da cewa yana son masoya shugaban su tura kudin ne domin nuna cewa har yanzu yana da masoya sabanin yadda wasu ke cewa masoyansa sun guje shi.
An samu sama da Naira miliyan 70?
A wani bayani da Aminiya ba ta iya tantancewa, an ce yanzu asusun ajiyar mawakin na bankin Zenith ya samu sama da Naira miliyan 70 a matsayin gudunmuwa.
Amma binciken Aminiya ya gano cewa tuni mutane da dama suka fara tura kudin, inda wasu suke tura Naira dubu daya din, wasu suke tura sama da hakan.
Kungiyar Muryar Talaka, ta hannun shugabanta, Alhaji Zaidu Bala Kofa Sabuwa, ta aika wa Rarara da Naira dubu 100.
Aminiya ta kuma ga wasu shaidun tura kudi da ke ta yawo a shafukan sada zumunta, inda mutane da dama suke nuna cewa sun tura kudin ga mawaki Rarara.
‘Da mu ba Rarara, gara mu kona kudinmu’
A wani bangaren kuma, Aminiya ta ga bidiyon wasu fusattun matasa suna koke-koken nuna rashin jin dadinsu kan yadda ake tura wa mawakin kudin.
Matasan, wadanda suka fito suna yagawa tare da kona kudin, sun ce da su tura wa Rarara gara kawai su yaga.
“Wallahi da in ba Rarara kudina gara in kona,” inji wani matashi a cikin wani bidiyo da Aminiya ta gani.
Wasu na yabo, wasu na suka
Kasancewar ana ta tura kudade, kuma ana yada shaidar turawa, sai lamarin ya haifar da cece-kuce da muhawara mai zafi.
Mutane da dama suna ganin bai dace a tura wa Rarara kudi ba don ya yi wa Shugaba Buhari waka, kasancewar yana da kudi.
Wasu kuma suna ganin ai za a tura kudin ne domin soyayyar Shugaban Kasa Buhari.
Kona kudin ya fi laifi
Wani mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum, Ibraheem Waziri cewa ya yi, “Akwai mutane da yawa daga cikinmu da suke ganin ba Shugaba Buhari ba ne kadai ke da laifi a tabarbarewar tattalin arzikin kasar.
“Haka muna tunanin bai kamata a rika daura masa duk laifin matsalolin da muke ciki ba yanzu.
“Amma Buhari ya kusa ya fara cancantar duk abin da aka jefe shi da su matukar mataimakansa suka bar Rarara ya ci gaba da neman kudi Naira dubu-dubu daga masoya Buhari domin ya masa waka.
“Sanin kowa ne ana cikin wani hali yanzu. Kamata ya yi Shugaba Buhari da mataimakansa su dage wajen tausasa mu, ba wai su koma gefe suna waka ba, sannan suna neman mu dauki nauyin hakan, shi kuma ya yi shiru yana kallo.
“Maimakon haka, kamata ya yi Rarara ya yi wa masoyan waka na jajircewarsu”, inji shi.
Wasu kuwa cewa suke yi ai gara ma wakar Rarara da wadanda suka tara wa Erica makudan kudi kawai don an cire ta daga cikin shirin BBNaija da ake yi yanzu.
An samu sabon salo
Bayan bukatar Rarara ta a turo masa kudi domin waka, an samu wasu mawaka da dama da suka biyo sahunsa.
Fitaccen mawaki Adam A. Zango shi ma a wani bidiyo da ya fitar, ya bukaci masoyan Jam’iyyar PDP da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar da su tura masa kudin da ya wake gwaninsa da waka mai taken ‘Atiku dawo 2023’.
Shi ma wani matashin mawaki Nura Karmatako ya ce zai yi wa Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari waka, inda ya bukaci masoya Masari su tura masa Naira 200 domin yin wakar.