✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda nake wayar da kan masu cutar – Mai kanjamau

Yaya kike tafiyar da masu dauke da kwayar cutar kanjamau? Da farko muna nuna wa mai dauke da wannan cutar ce cewa rayuwa tana dauke…

Yaya kike tafiyar da masu dauke da kwayar cutar kanjamau?

Da farko muna nuna wa mai dauke da wannan cutar ce cewa rayuwa tana dauke da jarrabawa kuma don mutum ya kamu da cutar ba shi ne karshen rayuwarsa ba.

Daga lokacin yaya kuke yi da sabon kamuwa da cutar?

A lokacin ne muke ba da shawara kan yadda mutum zai doru a kan shan magani domin idan mutum yana shan magani kuma yana cin abinci mai gina jiki zai samu sauki ta yadda wannan abinci da maganin zai yaki cutar, amma da zarar mutum ya ki shan magani a nan ne ake samun matsala har garkuwar jikin mutum ta karairaye.

Kuna samun wadanda suke bijirewa su ki yarda suna dauke da cutar?

Ko a watan Nuwamban bara, mun samu wanda ya ce bai yarda yana da cutar ba bayan an gwada shi an tabbatar yana da ita, saboda yana son auren wata yarinya da ba ta da ita. Muka yi, muka yi, amma ya ki wai shi dai sai ya aure ta, ita ma har ta amince masa a kan za su yi aure shi ne muka sanar da iyayenta suka hana auren.

Wannan kokari naki ana biyanki ne ko kina yi ne domin sa-kai?

Ba a biyana, aikin sa-kai nake yi bisa ga kokarina a bara 2017 har lambar yabo Hukumar Yaki da Cutar kanjama ta Jihar Gombe (GOMSACA) ta ba ni wanda hakan ya sa Kwamishinan Lafiya ya yi min alkawarin aiki, amma har yanzu shiru.