Nakasassu da tsofaffi sun samu kula ta musamman a aikin Hajjin bana.
Nakasassun da ba mu iya tantance adadinsu ba daga cikin alhazai sama da miliyan biyu daga kasashe daban-daban ne suka sauke farali a bana.
- WHO ta tallafa wa yara 6,000 da abinci mai gina jiki a Borno
- Dalilin da mutane ke komawa amfani da magungunan gargajiya
“An kebe musu wurin yin Sa’ayi a tsakanin hanyar tafiya Safa da Marwa ko dawowa, a kasa da kuma saman bene,” in ji Alhaji Aminu Muhammad.
Bayanai sun ce Ma’aikatar Aikin Hajji da Umarah ta Saudiyya da hukumomin tsaron kasar da sauran masu ruwa-da-tsaki a harkar sun yi ta tattaunawa kan yadda za a samar wa nakasassun masaukai da sauran abubuwan bukatunsu na yau da kullum a wuraren aikin Hajji da sauran wuraren ibada domin tabbatar da ganin sun samu isasshiyar kulawa mai inganci, ta yadda za su gudanar da ibada a cikin sauki a aikin Hajjin bana da aka kammala.
Ma’aikatar ta yi kebabben tsarin kula da lafiyar nakasassun alhazai, ta tanadi masu yin tafinta ga kurame, gami da bayanan da ake wallafawa da rubutun makafi.
Alhazan sun samu wannan kulawa ta musamman ce karkashin shirin saukaka wa nakasassu da marayu don yin aikin Hajji cikin walwala.
An fara aiwatar da tsarin ne a shekarar 2021 da alhazai nakasassu maza da mata 200 ’yan kasar Saudiyya, kafin adadin ya karu zuwa 300 a bara.
Hakan wani bangare ne na tabbatar da ingancin hudindimun da ake yi wa alhazai da kula da jin dadinsu a karkashin shirin cim ma burin kasar Saudiyya mai taken Bision 2030.
Manufofin shirin sun hada da bayar da karin muhimmanci ga nakasassu da bayar da karin dama a dama da su a cikin al’umma.
A yayin aikin Hajjin bana, an sama wa alhazai nasakassu tsarin sufuri na musamman gami da kebe musu hanyoyi domin su samu saukin aikin Hajji, wanda daya ne daga cikin rukunan Musulunci.
Kazalika an ware musu matakalar zamani a Masallacin Harami, domin zuwa ban-daki da wurin yin alwala ko hawa bene domin yin Dawafi ko Sa’ayi da sauran wuraren ibada.
Hasali ma, an gina ban-dakuna da wurin yin alwalar ne ta yadda nakasassu za su iya amfani da su cikin sauki.
Alhaji Aminu daga Jihar Jigawa ya ce duk da haka, “Ban-dakinsu daban yake, ba kamar sauran ba.”
“A Madina na shiga wani bandaki a wani otel, wanda a ciki na ga an tanadi kayan amfanin masu nakasa,” in ji Muhammad Sale daga Jihar Kaduna.
Akwai kuma kekuna masu amfani da wutar lantarki da aka tanada musamman a Masallacin Harami dominsu da kuma tsofaffi.
“Kananan motocin kwallon golf da aka tanada domin ayyuka a cikin masallatan biyu da harabarsu, sukan ba da fiffiko wajen rage hanya ga tsofaffi,” in ji wani Alhaji daga Abuja.
Wadannan tsare-tsare, ma’aikatar ce take aiwatar da su, da hadin gwiwar kungiyoyin jin kai da gwamnatoci.
A Masallacin Manzon Allah (SAW) da ke Madina, inda alhazai sukan kai ziyara, an tanadi kekunan guragu da masu bukata za su iya dauka su yi amfani da su kyauta, bayan sun bayar da takardar fasfo dinsu – idan sun dawo da keken sai su dauki fasfonsu.
Wani Alhaji daga Jihar Kaduna ya ce, “Tun washegarin da muka je Madina muka karbi keken guragu a masallacin, na ba da fasfo dina, sai da muka gama amfani da keken muka mayar na dauki fasfon dina.”
Sannan kusan a kowane bangare, daga Masallacin Manzon Allah har zuwa Masallacin Harami an tanadi kananan kujeru na musamman ga masu lalura, da za su yi amfani da su a kyauta.
Haka kuma a masallatan biyu masu alfarma, an tsara kofofinsu ne ta yadda shiga haraba ko cikin masallacin ko wani bangare nasa zai yi musu sauki.
Hakazalika jami’an tsaro da sauran ma’aikata sukan ba da muhimmanci wajen kula da nakasassu da masu rauni, kamar tsofaffi da sauransu.
Wani lokaci ma, har rakiya suke musu, ko su tallafa musu.
Kulawar da tsofaffi suka samu
Aminiya ta ga yadda wani jami’in tsaro a Masallacin Harami ya kai wani tsoho cikin inuwa daga cikin rana a harabar masallacin, a wata ranar Juma’a da zafin rana ya kai maki 50 a ma’aunin Celsius.
Ranar Arfa da aka je Muzdalifa, tsofaffi da mata aka fara kwashewa zuwa Mina, domin fara yin jifa.
A ban-daki a Mina kuwa, layi na yawa, amma idan suka ga tsoho, ko ya yi musu magana suna bari ya fara shiga.
A Masallacin Madina kuwa, kananan motocin da ake gudanar da aiki da su a harabar masallacin sukan dauki tsofaffi su kai su inda suke so.
Su kansu alhazai a tsakaninsu sukan ba da fiffiko ga dattawa.
Wani dattijo, Alhaji Musa Isa ya ce, “Ina cikin tafiya a rana bayan mun gama jifa a hanyarmu ta zuwa Makkah, wata ta miko min lema.”
A asibitin alhazan Najeriya da ke Unguwar Shara Mansur a Makkah, sau tari alhazan da suka je ganin likita sukan yi hakuri a fara duba tsofaffi da wadanda aka kawo su ranga-ranga, ba tare da sun yi jira ba.
“Koda ba su riga ka ba, bai kamata da tsufarsu mutum ya ce sai sun bi layi ba, saboda takamar cewa ka riga su.
“Akalla ko yanzu dattijuwa ta zo, ai ba sai ta roka ba, mutum ya san ya kamata ya bari a fara duba ta,” in ji wani Alhaji da ya bar wata dattijuwa da ta zo a bayansa ta fara ganin likita.
Wani matashi da ke zaune da wasu dattawa ’yan Najeriya, ya ce “Ba na jira, da zarar na lura lokacin abinci ya yi, zan je in karbo na duka ’yan dakin.
“Idan za su yi sayayya ina raka su, in dauko musu, kuma ina taya su wurin yin ciniki da zabar wanda ya dace.
“Idan muna hanyar Masallacin Harami da su, nakan lura da yanayinsu, wani lokacin har in matsa cewa mu tsaya a huta a hanya kafin mu ci gaba da tafiya, kuma suna jin dadin hakan,” in ji shi.