✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da mutane ke komawa amfani da magungunan gargajiya

Wasu za su ce sun sha maganin gargajiya kuma sun samu sauki, amma na Bature ba ya yi musu aiki.

A watan jiya ne Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta kama fitaccen mai harhada magungunan gargajiyar nan, Alhaji Salisu Sani, wanda aka fi sani da Baban A’isha.

An kama shi ne bisa zargin harhada magungunan gargajiya a wurin da bai dace ba da kuma amfani da lasisin da ya kare aiki.

Da take jawabi ga manema labarai a Abuja, Shugabar Hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye ta ce an kama shi ne saboda talla da kuma sayar da magungunan ba bisa ka’ida ba.

Ta ce a kwanan ne hukumar ta yi nazari a kan wani rahoton korafi da wata kafar yada labarai ta wallafa a kan magungunan da Baban A’isha ke sarrafawa.

Farfesa Adeyeye ta ce rabon da Baban A’isha ya sabunta lasisinsa tun a shekara ta 2020 saboda bai cika ka’ida ba, alhalin ya kare tun a shekara ta 2018.

Ta ce sakamakon yawan korafe-korafen da ake yi a kafafen sada zumunta na zamani, sashen bincike da tabbatar da bin doka na hukumar ya yi nazari tare da daukar matakin da ya kai ga rufe kamfanin da ake sarrafa maganin da kuma kama biyu daga cikin ma’aikatansa.

Shugabar ta NAFDAC ta ce sun fara aikin binciko masu sarrafawa da sayar da jabun magungunan gargajiya a sassan Najeriya.

Kamen na Baban A’isha ya biyo bayan wani rahoton binciken kwakwaf, inda aka gano bai sabunta lasisinsa ba, sannan gwaje-waje sun nuna akwai matsala a cikin maganin.

Wannan ya sa Aminiya ta dada binciken tare da kara bin diddigin wasu daga cikin magungunan.

Dokta Abubakar Garba Gailo wani mai maganin gargajiya da ya shahara tare da bude asibitinsa na farko a Jos kafin ya dawo Abuja inda ya bude asibitin a garin Gwagwalada, wanda dan asalin Karamar Hukumar Hadeja ce a Jihar Jigawa ya shaida wa Aminiya cewa ya shafe sama da shekara 30 a harkar tare da samun takardun shaida da kuma lambobin yabo a kai.

Daga cikin magungunan da ya ce yana hadawa akwai na cutar HIV da ciwon sanyi da asma da ciwon sukari da hawan-jini da ciwon daji da na koda da na hanta da sauransu.

Ya ce magangunan gargajiya sun saba da na Bature inda ya ce suna yakar cuta daga tushe maimakon dakatar da ita kadai.

Ya ce idan aka dace za a kauce wa yanke kafa ko wata gaba ta marar lafiya a dalilin kamuwa da cuta.

Ya ce ba daidai ba ne kai marasa lafiya kasashen ketare, alhali akwai magungunan gargajiya na cututtukan a gida.

Ya ce asibitin maganin gargajiya na farko da ya bude a Jos ya tafiyar da shi ne ta hanyar zamani kama daga tsarin fita na ma’aikata sama da 10 da ke aiki a karkashinsa zuwa tafiyar da aikin ga majinyata kan tsari na kundin bayani na fayel ga masu ziyartar wajen.

Dokta Abubakar Gailo ya ce sai dai a karshe ya rufe wajen ya tare a Abuja inda ya bude asibitin a lokacin tsohon Shugaban Kasa Janar Sani Abacha.

Ya ce hakan ya biyo bayan yawan tarurrukan masu maganin gargajiya da kuma yin nazari a kan magungunansu da aka rika yi a lokacin waccan gwamnatin.

“A lokacin an gudanar da bincike a kan maganin kanjamau da na samar a Cibiyar Binciken Magunguna ta Kasa (National Institute for Pharmaceutical Research) da ke Idu a Abuja.

Da yake bayani kan kalubalen da ya fuskanta a harkar, ya ce babban da ba zai manta ba shi ne na barazanar jingine binciken a kan magungunansa da kwamitin da gwamnati ta kafa a kai ya yi don tantance sahihancinsu, bayan ya ki amincewa ya bayyana sirrin yadda yake hada daya daga cikin magungunan (formula).

Ya koka kan yadda dangin wasu da ke da cutar kanjmau suka rika barinsa da alhakin kula da majinyatan bayan sun nemi izinin komawa gida su nemo kudin jinya.

“Wasu daga cikin dangin kan yi watsi da majinyatansu da suka kawo mini bayan na yi masu bayani a kan kudin da za a bukata inda suke ganin biyan kudin a matsayin rakiyar asara ce kan ba lallai ba ne maganin ya yi aiki.

“Sai dai in tausaya haka nan in yi wa mutum aiki.

“Akwai kuma masu karyar cewa su yarana ne, suna yawo da magunguna a kasuwanni, alhali maganina ba na yawo ba ne, ba ka samunsa a ko’ina sai idan Allah Ya kawo ka nan.

Ya ce yana gudanar da aikinsa ta hanyar hada kai da likitocin zamani.

“Ba na yarda in fara yi wa marar lafiya aiki sai an yi masa gwaji a asibitin gwamnati kan cuta da ta kawo shi.

“Sannan bayan na ba shi magani ya fara sha, sai a sake yin gwajin a can don tantance yanayin aikin maganin,” in ji shi.

Ya ce daga cikin magungunan da yake bayarwa akwai mai suna Coursecopler da Chedid da Habib da Ghose sai Zogale da ake ba da shi kai-tsaye ga wasu cututtuka irin hawan jini.

Ya ce magungunasa akwai na gari da na allura da ke cikin kananan kwalabe.

Ya ce kamar na kanjamau (HIV) da ke cikin kwalbar ruwan allura ana yin sa ne ga majinyaci duk bayan mako biyu inda ake ba da kasa da milgram daya na ruwan allurar a jijiya.

Ya ce tsawon lokaci da majinyaci zai yi amfani da maganin ya danganci girman cutar, inda yake kamawa daga watanni zuwa shekara guda.

‘Dalilin da muka fi gamsuwa da maganin gargajiya’

Malam Abubakar Muhammad mazaunin garin Kubwa a Abuja ya ce ya fara amfani da maganin gargajiya ne tun yana karami.

Ya ce ya zabi ci gaba da amfani da shi ne kasancewarsa na asali, sabanin na zamani wanda yawan amfani da shi ke haifar da matsaloli.

Ya ce wasu daga cikinsu abinci ne kuma ba sa da sinadarai da ke iya haifar da illa kan amfani da su.

Ya yi misali da wani ganye mai suna “rai-dore, da ya ce yana maganin zazzabin maleriya ko typhoid.

Ya ce yakan kirba ko ya dafa maganin, sannan a wani zubin yana amfani da shuwaka, sai ya warke.

Ya ce idan bai kai ga kwantar da shi ba kuma yakan yi amfani da shayin lemon grass da yake hadawa da sinadarin na’ana’a ya sha.

Ya ce bayyanar magunguna da ake kira Islamic Medicines ta kara wayar da kai kan adadin abin da za a yi amfani da shi.

Malam Abubakar ya ce idan aka bi ka’idar magungunan za a kauce wa fuskantar matsalar da daci ko bauri ke haifarwa da ake danganta shi da lahanta hanta.

Aminiya ta kuma tuntubi wani matashi mai suna Ibrahim Aminu wanda ke zaune a garin Kubwa Abuja, inda ya ce ya dauki kamar shekara shida yana amfani da maganin gargajiya.

Ya ce hakan ya biyo bayan wani ciwon ciki mai tsanani da ya yi ba tare da samun waraka ba ta hanyar amfani da maganin Bature, har sai da ya yi amfani da na gargajiya.

“Ko matsalar zazzabin cizon sauro na gamagari, maganin gargajiya nake amfani da shi, in samu sauki.

“Na shafe sama da shekara biyu ban yi amfani da maganin asibiti ba,” in ji Ibrahim.

Ya ce yakan yi sama da wata uku zuwa shida kafin ya sake haduwa da zazzabi.

Sai dai ya ce yakan yi amfani da bauri da daci a kai-a-kai don maganin zafi da maiko kamar duk bayan kwana uku.

Matashin wanda yake sana’ar dinki ya ce bai san matsalar cutar basir ba a rayuwarsa duk da kamar sa’a 20 da ya ce yana yi a zaman aiki, a wasu lokuta.

Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya gano kasuwar maganin gargajiya kara bunkasa take a Jihar Kano, musamman a tsakanin mata.

A ziyarar gani-da-ido da wakiliyarmu ta kai wurin masu magungunan gargajiya da ke daura da kofar Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, ta gano yadda mutane, musamman mata talakawa da attajirai ke tururuwar zuwa karbar magungunan yara da manya, da kaciya da kaho, da sauransu.

Wata mata da ta tarar ta je karbar maganin, ta ce likita ce ta ba ta shawarar zuwa wajen masu maganin gargajiyar don babu maganin asibitin da zai magance larurar danta.

Wata mata da ta kai danta kaciya ta bayyana wa Aminiya cewa duk da sukan je asibiti, ta lura na gargajiya ya fi aiki cikin sauri kuma yadda ya kamata.

“Da ina dari-darin zuwa nan, amma tun lokacin da dana ya yi wasu kuraje muka dinga zuwa asibiti muna karbar magani amma ya ki warkewa, sai na yanke shawarar zuwa nan tunda sanannu ne tun shekaru da dama.

“Ina zuwa kuwa aka ba ni maganin da ya warkar da shi ko tabo babu, kuma da kudin da ko kashi daya na wanda muka kashe a asibiti bai kai ba,” in ji ta.

Wata Hajiya A’isha da ta je karba wa jaririnta maganin yaye, ta ce zuwanta karbar maganin na uku ke nan.

“Kin ga lokacin yayen dana na farko na sha wahala sosai, don sau biyu muna hakura da yayen saboda kuka.

“Don haka da nake bai wa wata kawata labarin fargabar yaye na biyu, sai ta ba ni shawarar in zo nan suna ba da magani.

“Da na ki, amma da ya dame ni sai na zo, abu kamar asiri tunda ya fara sha sai ya daina,” in ji ta.

Ba da ka muke ba da magani ba — Wanzamai

Adamu Kawu, wanzami ne da ya shafe shekara 32 yana wanzanci a tsallaken Asibitin Malam Aminu Kano, ya ce ba da ka suke aikinsu ba, horo suke samu wanda ko likitocin ba sa samun irinsa.

“Kin ga zan iya ce miki a cikin wanzanci aka haife ni, domin tasowa na yi a gidanmu ina yi, kuma muna da kwarewar sanin magunguna da ake kira lakani a cikin gida da suka hada da ba da magani ga manya da mata da kananan yara.

“Na manya kin ga shi ne kamar cutar sabarar cikin jini, sanyi, na yara Ela (da aka fi sani da rana),” in ji shi.

Haka ya ce samun karuwar matan da suke zuwa wajensu neman magani kadai ya isa ya nuna kuskuren wasu likitoci na cewa maganin cutar da mutane yake saboda ba da shi ake yi babu ka’ida.

Ya ce, “Abu ne da yake a bude, tunda kika ga jama’a sun raja’a a kai, kin san ana ganin waraka ne.

“Wani za ki ga tun tsawon shekara 40 na zuwa wajen iyayenmu har ga shi mun taso na ci gaba da saya a wajenmu, ke nan da ba sa samun waraka ba za su zo ba.

“Sannan akwai sauki, domin ba ma sa farashi sai abin da aka dauka aka ba mu. Haka muka taso iyaye da kakanninmu na yi.

“Dalilinsu kuma shi ne kudin motar da mutum ya kashe ya zo wajenmu ya ishe shi.

“Amma AlhamdulilLahi duk da haka ga shi muna samun riba fiye da tunanin mutane.”

Dangane da zargin da ake yi cewa suna ba da magunguna ba ka’ida kamar yadda na asibiti yake, ya ce wadanda ba su san yadda suke ba da maganin ba ne ke yada wannan jita-jita.

“Duk wanda kika ji yana yada irin wadannan maganganu to bai san harkar ba.

“Farfaganda ce kawai ta masu son kushe duk wani abu da ba na Turawa ba.

“Iyaye da kakanninmu duk shi suka sha, mu ma shi suka ba mu, kuma ba a taba samun matsalolin da suke cewa ana samu ba.

Ya ce, “Magugunan da muke bayarwa na da ka’ida da tsari idan ka fada mana cutar da ke damunka mun san maganin da ya kamata mu ba ka da iya adadin kwanakin da ya kamata ka yi amfani da shi.

“Bayan magani kuma muna cire beli, ga kaciya, ga maganin kuraje.

“Bari in ba ki misali su kansu kurajen muna da ilimi a kan iri-iri ne, akwai wanda ya ja ruwa da ba a sa magani sai an fitar da ruwan da ya ja, akwai wanda sai an fara sa magani kafin a fitar.

“Akwai wanda magani kawai za a sha ba bukatar a fasa shi, haka akwai wanda idan aka bari ya fashe da kansa matsala ce.”

Dangane da yanayin ciniki wani mai ba da maganin gargajiya mai suna Idi Wanzam ya ce cinikin da suke samu a baya-bayan nan, ya ninka na shekarun baya.

“Gaskiya ana samun kasuwa a baya-bayan nan sosai, domin kin ga ranar da kasuwa ba ta yi kyau ba, a samu abokan hulda 20.

“To ranar zan ce miki gaskiya yau ba mutane, wanda a da shi ne ma alamar an samu kasuwa.

“Sannan da yara kadai aka fi zuwa nema wa magani, amma yanzu manyan ma na karba, musamman na basir da sanyi,” in ji shi.

Akwai masu illa ga koda da hanta — Likita

Khalifa Abdullahi Usman likitan yara ne a Jihar Kano ya ce duk da cewa masu ba da magungunan kan hada da na Bature su bayar a matsayin maganin gargajiya wasu suna da illa ga lafiya.

“Masu zuwa wurin mutanen nan za ki ga yawanci mata ne, kuma suna zuwa ne saboda ya fi araha idan kika kwatanta da na asibiti.

A asibiti sai an yi gwajegwaje wasu masu tsada ne sosai, kuma watakila ma a gama ba a gano mece ce matsalar ba.

“Amma magana ta gaskiya shi ne magungunan da ke cikin na Baturen nan akwai su a na gargajiya amma fa sun yi karfi da yawa, kuma ba a tace su ba.

“Misali wasu za su ce sun sha maganin gargajiya na ciwon sukari kuma sun samu sauki, amma na Bature ba ya yi musu aiki, kuma ba haka ba ne.

“Yawanci masu maganin gargajiyar nan suna samun na Bature ne su daka shi ya koma gari su hada da wasu abubuwan su bayar a matsayin na gargajiya shi ya sa za ka ga ya yi aiki.

“Dalili na biyu shi ne maganar idan ka yarda da abu ya yi tasiri. Shi ya sa shi ma Baturen ai ya zo da zauren tattaunawa ga marasa lafiya.

“Saboda idan mutum ya samu mai sauraron matsalolinsa, yana samun sauki ko bai kai ga shan magani ba,” in ji shi.

Dokta Khalifa ya kuma gargadi al’umma kan shan magungunan gargajiya musamman saboda rashin tsafta, da tace shi, hadi da rashin tabbas kan abubuwan da suke sarrafa maganin da shi.

“Yawanci za ki ga wadanda ake kawowa asibiti da larurar koda ko hanta, zai yi wuya bayan bincike a gano ba magungunan da suke sha ba ke nan.

“Saboda ita koda ita ke tace magani, don haka dura mata shi ba ka’ida lahanta ta yake yi ita da hanta.”

Khalifa ya musanta batun cewa likitoci na shawartar marasa lafiya su je wajen masu ba da maganin gargajiya a ko’ina a Najeriya.

“Maganar tura marasa lafiya su je wurin masu ba da magungunan gargajiya ba gaskiya ba ce, domin mutane ba sa tantance likitoci da sauran ma’aikatan lafiya da ba aikinsu ba ne ba da magani ko rubuta shi. Shi ya sa ake samun wannan jita-jitar.”