✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Arsenal ta cefano dan wasan bayan Ajax, Jurrien Timber

Arsenal ta yi cefanen dan wasan kan fam miliyan 34.

Arsenal ta kammala ɗaukar ɗan wasan baya na Ajax, Jurrien Timber kan kuɗi fan miliyan 34.

Ɗan wasan, ɗan asalin ƙasar Netherlands, mai shekara 22 ya sanya hannu kan kwantaragi na tsawon shekaru.

Zai ƙara wa bayan Arsenal ƙarfi, bayan da ɗan wasan baya na Arsenal, William Saliba ya amince da tsawaita zamansa a kulab ɗin da shekara huɗu.

Mai horas da Arsenal, Mikel Arteta ya ce: “Mun yi matuƙar farin ciki da sayen Jurrien. Matashin ɗan wasa ne mai basira.”

“Jurrien matashin ɗan wasa ne amma ya samu nasarori masu yawa. Yana da ƙwarewa na zuwa gasanni na duniya fiye da sau ɗaya, kuma ya lashe kofuna a Ajax.”

Timber na iya wasa a tsakiya ta baya ko kuma ta gefen dama, kuma a baya an alaƙanta shi da tafiya Manchester United, kuma Bayern Munich ta nuna sha’awar ɗaukansa.

Timber ya ce: “na daɗe ina son Arsenal.”