Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Manchester City da Arsenal sun yi kunnen doki a wasan mako na 30 na gasar Firimiyar Ingila.
Man City ta karɓi bakuncin Arsenal da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar Lahadi, sai dai mai masaukin baƙi ba ta samu nasarar doke Arsenal ba.
- Karin kudin kujerar Hajji ya dama wa maniyyatan Najeriya lissafi
- Yin Sallar Tahajjud a gida ya fi lada —Sheikh Ibrahim Khalil
Hakan na nufin ƙungiyoyin biyu sun raba maki a tsakaninsu.
Yanzu haka ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool ta koma mataki na ɗaya a gasar da maki 67.
Arsenal kuma ta koma mataki na biyu da maki 65, sai Manchester City mai riƙe da kambun gasar a mataki na uku da maki 64.
Ɗan wasan bayan Manchester City, Natthan Ake ya samu rauni a minti na 26 da fara wasan, yayin da Bukayo Saka na ƙungiyar Arsenal, ya samu rauni a minti na 77.
Yanzu haka dai wasanni tara ne suka rage a kammala gasar Firimiyar Ingila, kuma ana kyautata zaton tsakanin Liverpool, Arsenal da Manchester City wata ƙungiya za ta lashe gasar.